Labarai

Saboda rainin wayau daya daga cikin wandanda nake jagoranta limanci a masallaci ya ke buga harka da matata

Kotun grade one dake Mopo a Ibadan ta warware auren shekara 20 tsakanin wani limami Lukuman Shittu da matarsa Fisayo saboda rashin kauna da zargin zina.

Shittu ya roki kotun da ta raba auren sa saboda zinan da matarsa ke yi na bata masa rai sannan baya kaunar Fisayo a matsayin matarsa kuma.

Ya ce matarsa Fisayo ta canja a lokacin da ya talauce da har bashi da kudin da zai bata domin ta kama shago.

“Fisayo ta yi min karyar wai yan uwanta sun siya mata mota, ashe karyar banza ne, bayan na yi bincike sai na gane cewa ashe wani saurayinta ne da suke buga haraka ya siya mata.

Shittu ya ce tun da ya talauce Fisayo ta rika zuwa gida da dare, ta kwashe ‘ya’yan su uku da suka haifa tare daga gidan sa.

“Fisayo ta canja wa karamin yaron mu makaranta sannan ta sa sauran guda biyu ba za su rika gani na a matsayi mahaifinsu.

“Ya alkali na gano cewa saurayin Fisayo na sallah a masallacin da nake limanci.

Ita kuwa Fisayo ta ce Shittu bashi da mutunci sannan kulun yana yi wa rayuwarta barazana.

Ta ce Shittu ya zuga ni na ciyo bashi daga banki domin in fara sana’a amma sai ya yi amfani da kudin.

“Shittu ya rusa shago na wanda na kama da kudi na domin hana ni kasuwanci.

Alkalin kotun S.M. Akintayo ya raba auren saboda rashin kauna tsakanin ma’auratan.


Source link

Related Articles

8 Comments

 1. Great blog right here! Additionally your website
  so much up very fast! What host are you the usage
  of? Can I am getting your associate hyperlink to your host?
  I wish my website loaded up as quickly as yours lol

 2. Good day very cool web site!! Guy .. Excellent
  .. Amazing .. I will bookmark your site and
  take the feeds also?I am satisfied to seek out so many
  useful information here within the post, we want develop extra strategies on this regard, thanks for
  sharing.

  My blog post: Recycled Wood

 3. Hi, Neat post. There’s an issue together with your site in web explorer, might check this?

  IE nonetheless is the market chief and a huge part of other people will omit your fantastic writing due to this
  problem.

  Feel free to visit my blog photo printer

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button