Labarai

SABON TARIHI A INGILA: Rishi Sunak, ɗan asalin nahiyar Asiya zai zama Firai Ministan Birtaniya

Rishi Sunak ɗan asalin nahiyar Asiya na shirin zama sabon Firai Ministan Birtaniya, bayan janyewar da abokiyar hamayyar sa Penny Mordaunt ta yi kafin ƙarfe 14:00 agigon GMT na cikar wa’adin janyewar.

Wannan ne karon farko a tarihin duniya da ɗan asalin wata nahiya ba Baturen asali ba zai zama shugaban Birtaniya.

Sunak zai zama Shugaban Jam’iyyar ‘Yan Ra’ayin Riƙau ta ‘Conservative Party’, bayan murabus ɗin da Firai Minista Liss Truss ta yi.

A bisa al’adar siyasar Birtaniya, duk wanda ya zama shugaban jam’iyya mai mafi rinjayen ‘yan majalisa, to shi ne zai zama Firai Minista kai-tsaye.

Sunak dai matashi ne mai shekaru 42, zai gaji Truss wadda ta yi murabus bayan ta yi kwanaki 42 kacal kan mulki.

Sunak ya yi kansulan Exchegmquer a ƙarƙashin mulki Boris Johnson, tsakanin 2020 da 2022.

Kamar yadda Johnson ya sauka ba shiri, ita ma Truss ta sauka bayan ɓullar badaƙala.

Abokiyar hamayyar Sunak ta bayyana janyewar ta, kuma ta ce ta na goyon bayan sa.

Birtaniya da sauran ƙasashen Turai sun shiga garari bayan ɓarkewar yaƙin Ukraniya da Rasha, wanda ya haddasa ƙuncin rayuwa da tsadar kayan masarufi a faɗin Turai.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button