Labarai

Sai APC ta naɗa Zulum ko El-Rufai mataimakin Tinubu, idan ana so ta samu ƙuri’u a Arewa

Wasu mambobin Masu Ruwa da Tsakin APC sun ja hankalin jam’iyyar cewa idan har ana son a samu ƙuri’u daga Arewa, to a naɗa ko dai Gwamna Babagana Zulum ko kuma Gwamna Nasir El-Rufai mataikakin takarar Bola Tinubu.

Shugaban ƙungiyar Abdullahi Aliyu ne ya yi wannan kiran a lokacin ganawar sa da manema labarai a Katsina, ranar Lahadi.

Ya ce idan ana maganar cin zaɓe, to tilas facsai an samu mataimakin da ya cancanta sannan za a iya samun tulin ƙuri’u daga Arewa.

An dai fitar da rahotannin da ke nuna cewa APC ta miƙa sunan Sakataren Tsare-tsaren APC na Ƙasa, Ibrahim Masari a matsayin mataimakin takara na wucin-gadi.

An miƙa sunan Bola Tinubu da na Ibrahim Masari ga INEC domin a cika wa’adin ranar da INEC ta ce kada a wuce na a miƙa sunayen ‘yan takara ba.

Kawai dai an haƙƙaƙe cewa Masari mataimakin takara ne na je-ka-na-yi-ka, za a cire sunan sa a maye gurbin sa da wanda ake so a naɗa daga baya.

“Mu na sane da cewa Zulum ya bayyana cewa niyyar sa ya cika wa’adin ayyukan da ya fara a Jihar Barno, ba ya buƙatar mataimakin shugaban ƙasa. To amma ai muhimmancin Najeriya ya fi na Jihar Barno.” Inji Aliyu Abdullahi.

“Mun san Bola Tinubu ɗan takarar da zai iya fidda kitse daga wuta ne kafin ya narke, amma fa ya na buƙatar mataimaki daga Arewa wanda shi ma ya yi ayyukan ƙwarai kuma an shaida hakan. Ta haka ne kawai za a iya samun amincewar jama’a daga Arewa su zuba wa APC ƙuri’u a zaɓen 2023.”

Aliyu ya ce idan kuma Zulum ya baɗa masu ƙasa a ido, to za su baza komar su don su kamo Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, su nemi a naɗa shi mataimakin takarar Tinubu.”

“Saboda mu shugabannin da su ka cancanta kaɗai mu ke so. Saboda idan ba waɗanda su ka cancanta ne su ka tsaya wa APC takara ba, mu na ji mu na gani Atiku Abubakar da PDP za su ƙwace mulki a zaɓen 2023.”


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news