Labarai

SAKACIN EFCC: Kotu ta wanke tsohon Minista Kabiru Turaki daga zargin wawurar kuɗaɗen da EFCC ta yi masa

A ranar Litinin ce Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta sallami tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Kabiru Turaki daga zarge-zargen karkatar da kuɗaɗe, wanda EFCC ta maka shi ƙara.

Mai Shari’a Inyang Ekwo ya zartas da hukuncin cewa EFCC ta kasa gabatar wa kotu da gamsassun hujjoji ko shaidun da za su gamsar da kotun cewa Kabiru Turaki da sauran waɗanda ake tuhumar sa tare, sun aikata laifuka 16 da EFCC ɗin ke cajin su a gaban mai shari’a.

Ya ce an buga, an kai, an kawo amma mai gabatar da ƙara ya kasa gamsar da kotu da hujjojin waɗanda ake zargin sun aikata laifukan da ake tuhumar su.

‘Masharranta EFCC Ta Gabatar A Kotu, Ba Masu Shaida Ba’ -Mai Shari’a Inyang Ekwo:

Mai Shari’a ya ce waɗanda ake ƙara sun ragargaji shaidu ko hujjoji 12 ɗin da EFCC ta gabatar, ta yadda kotu ta gamsu cewa hujjojin da EFCC ta gabatar ”kayan sharri ne, ba hujjoji ba ne.”

Kotu ta ce an yi zube-ban-ƙwarya a kotu, amma dukkan hujjoji ko shaidun da aka gabatar babu inda aka tabbatar da sa hannun Kabiru Turaki a Asusun Kuɗaɗen Ma’aikatar Ayyuka na Musamman, kuma babu inda ya rubuta cewa a biya wasu kuɗaɗen da ake zargin an karkatar.

Sannan kuma kotu tabbatar da cewa Turaki baya cikin hukumar kwamitin bayar da kwangila, sannan kuma babu inda kuɗi suka fita daga asusun Ma’aikatar Ayyukan Musamman su ka shiga
Asusun Kamfanin Turaki.

Idan ba a manta ba, EFCC ta zargi Kabiru Turaki da laifin karkatar da naira miliyan 715.


Source link

Related Articles

13 Comments

  1. Hi there, You have done an incredible job. I’ll definitely digg it and personally recommend to my friends.
    I am sure they will be benefited from this website.

  2. Spot on with this write-up, I honestly believe that this web site needs a lot more attention. I’ll
    probably be returning to read through more, thanks for the information!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news