Nishadi

Sarki Ahmed Bamalli na Zazzau ya dakatar da hakimai hudu

Mai Martaba Sarkin Zazzau Ahmed Bamalli ya dakatar da hakimai huɗu na Masarautar Zazzau daga muƙamansu saboda karya dokar masarautar.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Fadar Zazzau, Abdullahi Kwarbai ya fitar jim kaɗan bayan sauka daga hawan sallah, kamar yadda BBC Hausa ta buga, an dakatar da hakiman ne bisa karya dokokin da aka gindaya na Hawan Sallah wanda ke cikin kundin dokokin hawa a masarautar.

Hakiman da aka dakatar sun haɗa da Ubangarin Zazzau Alhaji Bashir Shehu Idris ɗan tsohon sarkin Zazzau marigayi Shehu Idris. Sai kuma Wakilin Birnin Zazzau Alhaji Suleiman Ibrahim Dabo wand shine ɗan majalisan jiha dake wakiltar birnin Zariya da Sarkin Dajin Zazzau Alhaji Shehu Umar da kuma Garkuwan Kudun Zazzau Alhaji Muhammadu Sani Uwais.

Ana zargin hakiman da saɓa doka ta uku da ke cikin kundin laifukka da hukunce-hukuncen hawa a Masarautar Zazzau wadda ta haramta wa kowane hakimi yin hawa da ƴan tauri riƙe da makamai.


Source link

Related Articles

4 Comments

  1. Filipinler’de ilaç dağıtım hizmetleri olan bu çevrimiçi eczaneler listesinden ilaçlarınızı satın alın. Popüler
    Mesajlar. Çocuğunuzun Öğrenim Fonu Oluşturma:
    Yeni Ebeveynler için 5 Adımlı Kılavuz. Ocak 2016’nın En İyi
    Kredi Kartı Promosyonları.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news