Labarai

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, Ya Zama Uban Kungiyar ‘Marubutan Arewa’ ( Arewa Media Writers) Na Kasa Baki Daya

A yau Laraba Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani ‘Arewa Media Writers’ karkashin jagorancin shugaban Kungiyar na kasa Abba Pantami, ta kai ziyara fadar mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, tare da kaddamar dashi a matsayin uban kungiyar na kasa baki daya (Grand Patron).

Wasu daga cikin shugabannin kungiyar na kasa sun halarci taron da shugaban kungiyar reshen Jihar Kano Umar Kabir Dakata, tare da sauran shugabannin kungiyar reshen jihar da Membobin Kungiyar da dama.

Kungiyar ta nada Mai Martaba Sarkin ne a matsayin uban kungiya na kasa dubi da irin gudunmawar da yake baiwa al’ummar yankin Arewa baki daya a matsayin sa na mai rike da sarautar gargajiya mai daraja, a wannan yanki namu na Arewa.

A yayin ziyarar Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, yayi maraba ga wannan Kungiya bisa Ziyarar data kawo masa kafa da kafa, sannan ya jinjinawa wadanda suka kafa kungiyar tare da yaba musu kan irin namijin kokarin da suka yi na kafa kungiyar.

Mai martaba ya kara da cewa ‘Social Media’ wato kafafen sada zumunta na yanar gizo wuri ne mai muhimmanci a wannan zamani namu, Sarki yace mafi yawancin jama’a hankalin su ya koma kan kafafen yada labarai saboda haka yayi kira ga wannan kungiya da ta cigaba da abubuwan da tasa gaba domin abubuwa ne masu kyau.

Sarkin yace, yana tare da wannan Kungiya kuma yayi alkawarin bata gudun mawa ta kowane fanni domin ci gaban yankin mu na Arewa.

A karshe mai martaba Sarki, ya yiwa kungiya fatan Alkhairi tare da fatan Allah ya kara daukaka ta.

A jawabin shugaban Kungiyar na kasa, Abba Pantami, ya mika godiya zuwa ga mai martaba Sarkin bisa amincewa da wannan kungiya da yayi, kuma ya karbeta hannu biyu biyu, sannan ya Godewa mai martaba Sarkin sakamakon yadda yake taimakon Arewa da yan Arewa baki daya.

Pantami ya yi wa Sarkin Bayero alkawarin ci gaba da jajircewa don ganin an samarwa da yankin Arewa ci gaba ta kowane fanni.

Haka zalika Kungiyar tayi kira ga Al’umma da su bawa kungiyar hadin kai tare da goyon baya domin kawo wa yankin Arewa da Najeriya baki daya ci gaba mai amfani.

“Kungiyar “Arewa Media Writers” tana bukatar Addu’o’i daga gareku Allah ya shige mata gaba kan muhimman ayyukan da ta saka a gaba. Amin” – Rokon Pantami.


Source link

Related Articles

71 Comments

  1. Incredible! This blog looks exactly like my old one! It’s on a entirely
    different topic but it has pretty much the same page layout and design. Superb choice of colors!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button