Nishadi

Sarkin yaƙin Atiku ya watsar da sarautar, ya tsinduma rundunar Tinubu da Uba Sani

Sarkin yakin rundunar ɗan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar a 2019 kuma jigo a farfajiyar Kannywood, Zaharadden Sani ya watsar da sarautar Sarkin Yakin Atiku ya tsinduma cikin APC.

Zaharadden Sani da ya tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA ya shaida cewa tuni har Jam’iyyar APC ta amshe shi hannu bibbiyu har an bashi matsayi a tafiyar Sanata Uba Sani, ɗan Takarar gwamnan jihar Kaduna.

Bayan haka ya bada dalilan da ya sa ya fice daga tafiyar Atiku sannan ya fice da ga PDP kwatakwata.

” Ba bubu wanda bai sanni cewa na yi wa Atiku aiki ba a PDP a 2019. Ko yanzu kafin na fice daga PDP, ni kadai na rage muhimmin mutum ɗan Kannywood. Duk kowa ya kama gaban sa saboda yadda rashin adalci da jam’iyyar ke nuna mana.

” Na gamsu cewa Atiku ba zai iya yin adalci ga ƴan kasa ba tunda gashi a haka ma ya kasa sa wa a yi abinda ya dace.

” Ni ɗin nan ina da magoya baya masu ɗan ɗinbin yawa, kuma tare da ni kaf din su muka tsinduma APC.Daga gobe zan fara fita kamfen gadangadan da tawagar APC kuma sai munga abinda ya ture wa buzu naɗi a wannan tafiya.

” In dai tafiyar Atiku ne ni Zaharadden na sallama da shi.


Source link

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *