Labarai

SHARI’A SAƁANIN HANKALI: ‘Yadda Ministan Shari’a Malami ya damalmala hukuncin kotu a kan Dokar Zaɓe’ -Femi Falana

Babban Lauya mai rajin kare haƙƙi da ‘yancin jama’a Femi Falana ya zargi Ministan Shari’a Abubakar Malami da damalmala Babbar Kotun Tarayya ta yadda ta bayar da hukunci baddalalle mai cike da tarnaƙi akan matsayar sashe na 84(12) na Sabuwar Dokar Zaɓe ta 2022.

Falana ya ce Malami ya yi bakam, ya nuna kamar bai ma san akwai wani hukunci ko umarnin kotu wanda na Kotun Tarayya wanda ya haramta masa yin katsalandan a kan dokar. Amma sai ya jajirce cewa shi sai ya yi amfani da umarnin Babbar Kotun Umuahia, wadda ta bayar da umarnin a soke wannan sashen ɗungurugum.

Falana wanda babban lauya ne (SAN), ya fitar da sanarwa inda ya bayar da cikakken bayanin yadda Manyan Kotunan Tarayya guda uku suka bayar da mabanbantan hukunce-hukunce. Daga nan Falana ya ɗora laifin gaba ɗaya a kan Ministan Shari’a Malami.

“Don haka sai Falana ya ce ya kamata Malami ya sani cewa ba fa zai iya yin yadda ya ga dama ba, ta hanyar bin umarnin da ya ga dama, kuma ya bijire wa wadda ya gada dama.

“Sannan kuma babu sauran wata jikara ko tantama, tabbas Ministan Shari’a ya damalmala hukuncin Babbar Kotun Tarayya har ta bayar da baddalallun hukunce-hukunce a kan sashe na 84(12) na Dokar Zaɓe ta 2022.” Inji Falana.

Malami Ko ‘Malam Karkata’: Yadda Minista Malami Ya Sa Kotunan Tarayya Su Ka Bayar Da Mabambantan Hukunce-hukunce A Shari’a Ɗaya -Femi Falana:

Idan za a tuna, a ranar 18 Ga Maris, Kotun Tarayya ta Umuahia a Jihar Abia ya soke Sabuwar Dokar Zaɓe Sashe na 84(12), wanda ta ce ya ci karo da wani sashe na Dokar Ƙasa. Wannan sokewa dai ya kasance an yi abin da Shugaba Muhammadu Buhari ke so kenan, wato a soke dokar.

Sashen dai ya haramta wa masu riƙe da muƙamai na siyasa su shiga zaɓe a matsayin wakilan ‘deliget’ yayin gangamin zaɓen shugabannin jam’iyya da sauran su.

Mai Shari’a Evelyn Anyadike ta ce wannan sashe na doka da ta soke, ba shi da hurumi a cikin kundin dokokin Najeriya, haramtacce ne, ba shi ma da wani amfani.”

Daga nan ta umarci Ministan Shari’a kuma Antoni Janar ya goge dokar a cikin daftarin dokokin Najeriya. Wato aka ce ya shafe Sashe na 84(12) na Dokokin Zaɓe na 2022.

Ta ce dokar ta ci karo da wani sashe wanda ya bai wa masu riƙe da muƙamai damar tsayawa takara, amma su ajiye muƙaman su ana saura kwana 30 kafin zaɓe.

Sai dai kuma lauyoyi da dama sun la’anci wannan matsaya ta soke wani sashe na doka.

Da ya ke a ƙarar da aka shigar tun da fari, har da Abubakar Malami aka gurfanar. Shi kuma Malami ya nuna shauƙin son ya soke Sabuwar Dokar.

Ko ba komai dai soke dokar zai taimaki malami a matsayin sa wanda zai tsaya takarar gwamnan Jihar Kebbi a zaɓen 2023.

Falana ya ce Malami ya wulaƙanta ofishin sa da muƙamin sa, saboda ya tafi ‘ya na shawagin-dibak-kaɗe’, don kawai ya sami wasu hukunce-hukunce da zai rataya a wuya, don ya soke dokar zaɓe ta Sashe na 82(12).

Idan kuma ba a manta ba, a ranar 8 Ga Maris, 2022 Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya ya bayar da hukunci a kan wata ƙara da PDP ta shigar a kan Dokar Zaɓe, tunda ta zama doka, cewa kada a kuskura wani Ministan Shari’a ya taɓa Dokar Zaɓe ko ya soke ta kwata-kwata.

Ba Abubakar Malami kaɗai kotun ta yi wa gargaɗin ba, har da Shugaba Muhammadu Buhari sai da kotun ta ce ko shi bai isa ya taɓa Dokar Zaɓe ta 2022 ba. Haka nan kuma ta gargaɗi Majalisar Tarayya da ta Dattawa.

Amma abin mamaki, kwanaki 10 bayan wannan hukuncin, yayin da aka taɓo batun a Babbar Kotun Tarayya ta Umuahia, sai labari ya sha bamban, kotun ta bayar da umarni ga Minista Malami cewa ya soke dokar.

A kan haka ne Falana ya nuna ɓacin rai ya ce Malami ya yi wa fannin shari’a tuƙin ganganci, ta hanyar ƙin sanar da Babbar Kotun Umuahia cewa akwai hukunce-hukunce biyu a baya waɗanda su ka hana a taɓa sabuwar dokar ko a soke ta.


Source link

Related Articles

8 Comments

 1. Hi, I think your blog might be having browser compatibility issues.

  When I look at your blog site in Chrome, it looks fine but when opening in Internet
  Explorer, it has some overlapping. I just wanted to
  give you a quick heads up! Other then that, awesome
  blog!

 2. Hello i am kavin, its my first occasion to commenting anyplace,
  when i read this piece of writing i thought i could also make comment due to this brilliant piece
  of writing.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news