Ciwon Lafiya

Shin da gaske ne wai wasu sun rika cin naman junasu bayan an yi musu Rigakafin Korona a wasu kasashe? – Binciken Dubawa

Zargi: Wani hoton da ake zargi ya fito daga gidan talbijin na CNN ne ya ce an rufe wasu asibitoci domin wadanda suka yi allurar rigakafin COVID-19 sunkashe juna sun ci naman jikinsu.

Bayan da aka fara allurar rigakafin COVID-19 a kasashe da dama ciki har da Ghana domin dakile yaduwar cutar coronavirus, wani hoton da ya yi kama da dakin tiyata da jini ko’ina na yawo a shafukan yanar gizo a kasar Ghana da wasu wurare daban, dauke da zargin cewa an kulle wasu asibitoci bayan da wasu wadanda aka yi musus allurar rigakafin COVID 19 sun kama juna suna kokarin cin naman juna. Ana zargin an dauki hoton ne sadda tashar CNN ke watsa labaranta kai tsaye.

Hoton, wanda wata mai amfani da shafin Twitter ce ta fara saka shi da wasa tana cewa nan da watan Yuni zamu fara yaki da dodanni.

Da DUBAWA ta gudanar da bincike a shafin google, ta gano cewa jaridar New York Times ce ta fara wallafa hoton ranar 14 ga watan Fabrairu 2019, kafin barkewar COVID-19. Labarin da aka wallafa tare da hoton, cewa ya ke yi matashin nan da aka harbe ya rasu a asibitin koyarwa ta jami’ar Temple da ke Amurka bayan da ma’aikatan lafiya suka yi iya kokarinsu wajen ganin sun ceto rayuwar sa.

Duk da cewa wadda ta fara saka hoton ba ta cire komai a ciki ba, DUBAWA ta lura da alamun kwaskwarimar da aka yi wa hoton domin ya dace da labarin wai cin naman mutane ake yi.

Dubawa ta yi amfani da manhajan Forensically – mai tantance sahihancin hotuna – dan tantance hotunan biyu, wato da wanda New York Times ta wallafa da wanda ta gani a shafin Twitter. Daga nan ne DUBAWA ta gano wasu daga cikin abubuwan da aka yi wa hoton dan ya dace da labarin. Misali, hoton bai fito da kyau ba, akwai wani abu yashi-yashi da ke hana hoton fita da kyau.

Idan har aka duba hotunan biyu da kyau, wato da wanda jaridar New York Times ta wallafa da wanda ke yawo a yanar gizo – za a ga banbancin dake tsakaninsu, har ma da abubuwan da aka gyara domin su dace da labarin da ake so a bayar.

Hakanan kuma babu wani hoto ko labari irin wannan daga CNN da ke cewa an kulle wani asibiti saboda wadanda suka fara karnar allurar rigakafin COVID-19 sun cinye juna. Sai dai an gano wata manhagar da ke taimakawa mutane su kirkiro hotuna da labarin da ka iya yaudarar jama’a. Wannan manhaja mai suna Media Photo Frames; Breaking News App Photo Editor na taimaka wa mutane su kirkiro labari su kuma yi amfani da wasu daga cikin abubuwan da halatattun tashoshin labarai ke amfani da su.

Bayan haka, a watan Disambar 2020 wannan hoton ya dauki hankali a wasu kasahen duniya banda Ghana, yana dauke da labari makamancin wannan amma tuni aka yi watsi da zargin. Kafofin tantance sahihancin labarai kamar DUBAWA suka tantance labarin kuma sun hada da Times of India, India Today da AFP.

A Karshe

Hoton da ke zargin cewa wadanda suka fara yin allurar rigakafi a Ghana sun ci naman juna karya ne. A watan Fabrairun shekara ta 2019 hoton ya fara fita, yana nuna daya daga cikin dakunan tiyatan da ke asibitin koyarwa na jami’ar Temple bayan da wani matashin da aka harbe ya mutu a wurin. Tashar CNN ba ta ruwaito wani labarin da ya ce an kulle asibiti saboda wadanda suka yi allurar rigakafin COVID-19 suna kashe juna dan su ci naman jikinsu ba.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button