Labarai

Shugaba Zelensky na Ukraine ya yi hatsarin mota

Wani Hatsarin mota ya rutsa da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky a Kyiv babban birnin kasar.

A wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban ya fitar ya ce wata motar fasinja ce ta daki tawagar motocin da shugaban ke ciki ranar Laraba a birnin na Kyiv.

Shugaban dai bai samu munanan raunuka ba kamar yadda likitansa ya bayyana.

Tuni dai aka yi wa diraban motar fasinjan magani, yayin da kuma daga bisani aka dauke shi a motar daukar masara lafiya

Hadarin ya faru ne bayan da Mista Zelensky ya ziyarci birnin Izyum da ke arewa maso gabashin kasar, wanda dakarunsa suka kwace daga hannun sojojin Rasha.

Daga BBC Hausa

The post Shugaba Zelensky na Ukraine ya yi hatsarin mota appeared first on VOICE OF AREWA.


Source link

Related Articles

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news