Labarai

Shugaban INEC na so Majalisar Tarayya ta sa himma kan yi wa dokar zabe kwaskwarima

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Mahmood Yakubu, ya yi kira ga ‘yan Majalisar Tarayya da su yi aiki ba tare da la’akari da jam’iyyar da kowanne ke wakilta ba wajen yi wa Dokar Zabe garambawul wanda zai taimaka wajen inganta yadda ake gudanar da zabe a Najeriya.

Yakubu ya yi wannan kiran ne a wajen bikin daddamar da kwamitin hadin gwiwar kwararru na yi wa Dokar Zabe kwaskwarima wanda aka yi a Abuja a ranar Juma’a.

Kwamitin Hadin Gwiwar Majalisar Tarayya kan Hukumar Zabe da Al’amuran Zabe ne ya shirya taron tare da tallafin Cibiyar Tsare-tsare da Aikin Doka, wato Policy and Legal Advocacy Centre (PLAC) da kuma Ofishin Harkokin Kasar Wajen Birtaniya da Cigaban Kwamanwal, wato UK Foreign and Commonwealth Development Office (FCDO).

Festus Okoye, wato Babban Kwamishinan INEC kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe a hukumar, shi ne ya wakilci Mahmood a taron.

Yakubu ya ce garambawul din ya zo a kan kari, kuma abu mafi muhimmanci shi ne lallai a tabbatar da cewa gyare-gyaren sun yi tasiri, kuma an yi su ba tare da kallon kowace jam’iyya ba, sannan a cire duk wata rarrabuwar kai, kuma a kammala su akalla daga yanzu zuwa watanni hudu na farko na shekarar 2021.

Idan an tuna, tun a cikin 2020 ne shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya yi alkawarin cewa Majalisar Tarayya za ta bada hadin kai wajen zartar da gyaran Dokar Zabe ya zuwa karshen watanni hudu na farko na shekarar 2021.

Shugaban na INEC ya yi na’am da sabon yunkurin da kuma sadaukarwar da shugabannin Majalisar Tarayya su ka nuna wajen yi wa tsarin dokokin gudanar da zabe kwaskwarima.

Yakubu ya ce sabon hobbasan da majalisar ke yi ya zo a kan kari kuma tilas ne a ci gaba da shi tare da aiwatar da shi a cikin tunanin waiwaye da kuma hanzari.

Ya ce lallai ne a tabbatar da yunkurin ya tafi bisa hanyar kammaluwar sa, hanzari, saka hannu da tunanin dabaru.

Yakubu ya ce hukumar ta sadaukar da kai sosai ga tabbatuwar aikin garambawul din kuma za ta ci gaba da bada shawarwari da za su taimaka wajen ingantuwar harkokin zabe a kasar nan.

Ya kara da cewa gyara tsarin dokokin zabe ba wai zai haifar da sauyi farat daya wajen aikin gudanar da aikin zabe ba.

Ya ce: “Tsarin Mulki da kuma Dokar Zabe ba su iya yin aiki da kan su, kuma dukkan su su na motsawa ne ta hanyar ayyuka ko rashin ayyukan masu ruwa da tsaki a tsarin zabe.”


Source link

Related Articles

5 Comments

  1. I loved aѕ muсh ɑs you’ll receive carried ouut rifht һere.
    Tһe sketch іs attractive, yⲟur authored material stylish.

    nonetһeless, yοu command geet bought ɑn shakiness over that you ԝish be delivering tһe folⅼowing.
    unwell unquestionably ϲome further formerly aɡаin as exactⅼy thе same nearⅼy a ⅼot often inside сase you shield tһis increase.

    Also visit myy blog Universitas Islami Terbaik di Jakarta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button