Labarai

Shugaban Jami’ar Maryam Abacha, Farfesa Gwarzo zai yi jawabi a jami’ar IHERIS dake kasar Togo

Shugaban rukunin jami’o’in Maryam Abacha (MAAUN) da Franco British international (FBIU), Farfesa Adamu Gwarzo, zai yi jawabi a wajen bukin ɗaukar sabbin ɗalibai da za a yi a jami’ar kasar IHERIS dake kasar Togo.

Farfesa Gwarzo wanda shine shugaban Kungiyar jami’oi masu zaman Kansu na Nahiyar Afrika (AAPU), na cikin Jeri manyan baƙi da aka gayyato da za su yi jawabi a wajen taron.

Farfesa Gwarzo sananne ne a al’amuran da suka shafi inganta harkar ilimi a Nahiyar Afrika.

Farfesa Gwarzo zai yi jawabi ne akan muhimmaci haɗin Kan jami’oi masu zaman kansu a Nahiyar Afrika tare da kawo sauyesauye masu ma’ana wajen tafiyantar da salon kawo ci gaba a jami’oi masu zaman kansu a nahiyar afrika ta hanyar bincike,tallafi, kirkiro da sabbin fannoni na kimiya da fasaha , karfafa a’laka a tsakanin shuwagabanin jami’oi.

ZTaron Kara wa juna sanin na salle De da farfesa Adamu Abubakar Gwarzo zai hallarta a ranar 30 ga Oktoba a cikin shekara 2021 a Eda -oba lome, a kasar Togo.

Shugaban rukunin jami’oi Maryam Abacha (MAAUN) da Franco British international (FBIU) Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, sananne ne a duniya musamman a kwazon sa na ganin an samu ci gaba a fannin ilimi a nahiyar Afrika da kuma baiwa talakawa damar ƴaƴan su su yi karatu ta hanyar agaji da tallafin karatu.


Source link

Related Articles

14 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button