Labarai

SIYASAR JAJEN AMBALIYA: Atiku zai karaɗe jihohin da su ka yi fama da ambaliya, bayan Tinubu ya je wa Kanawa jaje

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar zai fara rangadin zuwa jaje a jihohin da ambaliya ta fi yi wa mumnunar ɓarna.

Cikin wata sanarwa da Paul Ibe, Kakakin Yaɗa Labaran Atiku Abubakar ya fitar a ranar Asabar, ya ce Atiku zai fara ne da jihar Bayelsa.

“Zagayen jajentawar ya zama tilas, idan aka yi la’akari da irin ɓarnar da ambaliyar ta yi, da kuma halin taskun da ta jefa waɗanda ambaliyar ta shafe su.

“Saboda haka zagayen jajentawar zai bai wa Atiku damar ganin irin gagarimar ɓarnar da ambaliyar ta haifar, ta yadda hakan zai ƙara masa hasken yadda zai shata daftarin tsare-tsaren magance matsalar ta ambaliyar idan har ya yi nasarar zama shugaban ƙasa.”

A ranar Lahadi ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi ya kai ziyara jihar Bayelsa domin jajentawa kan mummunar ambaliyar da ta shafi jihar.

Haka kuma a ranar Asabar ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya je jajenta ibtila’in ambaliya a Kano, inda har ya bayar da tallafin naira miliyan 100 ga waɗanda ambaliya ta shafa a jihar.

Idan ba a manta ba, cikin watan Satumba Tinubu ya kai ziyarar jajentawa a jihar Jigawa dangane da ambaliya, har ya bayar da gudunmawar naira miliyan 20.

Haka kuma Atiku ya nuna ɓacin ran sa dangane da yawan hare-haren da ake kai wa mutane a jihar Benuwai.

Daga nan ya yi kira a daina rikice-rikicen ƙabilanci, bangaranci da sauran su.


Source link

Related Articles

One Comment

  1. Howdy, i read your blog occasionally and i own a similar one and i
    was just wondering if you get a lot of spam remarks?
    If so how do you reduce it, any plugin or anything you can advise?
    I get so much lately it’s driving me insane so any help is very much appreciated.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button