Labarai

TA KICIME A APCn KADUNA: Ɓangaren Sha’aban ba su amince da zaben wakilan jam’iyyar APC da aka yi ba

Ɗaya daga cikin waɗanda ke kan gaba wajen takarar gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar APC , Sani Sha’aban ya ƙalubalanci sakamaon zaben wakilan jam’y APC da aka yi a jihar Kaduna.

Darekta Janar din kamfen din Sani Sha’aban Joshua Ephraim ya bayyana cewa ba a gudanar da taron wakilai na APC a jihar Kaduna ba saboda haka suna kalubalantar sanarwar wai an yi taro irin haka kuma wai babu ƙorafi da wani bangare ya kawo.

Sun zargi jami’an hukumar zabe da ta kula da zaben da kantara karya cewa wai an gudanar da zabe sannan kuma kowa ya gamsu babu korafi ko ɗaya.

” Mutane da yawa ƴaƴan jam’iyyar mu sun cika fom ɗin zama wakilan jam’iyyar amma da gangar aka ki amsar fom din aka hana su da gangar.

” Kuma bayan haka mun aika da korafin mu ofishin hukumar zabe INEC a Kaduna. A ciki mun shaida musu cewa ba a gudanar da sahihin taron na wakilai a jihar ba da zabuka kamar yadda ɓangaren jam’iyyar cewa anyi.

” Saboda haka muna so mu sanar wa muku cewa ba a yi taro da zaben wakilai da za su yi zaben fidda gwani na gwamna a Kaduna ba. Kuma ga korafin mu nan mun aika wa INEC.

Ephraim ya ce suna yin kira ga hukumar zaɓe ta yi wancakali da rahoton wacce ta kula da zaɓen wakilan a Kaduna cewa an ɗirka mata buhunan Ghana Must Go ne da masu gidan rana, ta kantara karyar wai komai ya gudana lumui a Kaduna.

A jihar Kaduna akwai sanata Uba wanda shine zabin gwamna Nasir El-Rufa’i, sai kuma Honorabul Sani Sha’aban ne ke kan gaba a takarar gwamna a jihar karkasjin APC.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news