Labarai

TAKARAR SHUGABAN KASA: Muna tare da kai a koda yaushe – Sarkin Katsina Abdulmumini ga Osinbajo

Sarkin Katsina Mai martaba Abdulmumini Usman ya shaida wa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo cewa lallai suna tare da shi a koda yaushe

Mai martaba Abdulmumini ya ce ” Kasani yau muna tare da kai. Wanda ya ke da kwarewa ya fi sabon shiga. Wannan yana daga cikin dalilan da ya sa muke tare da kai a wannan tafiya.

” Ina yi maka fatan Alkhairi, kai mutum kamili mai hakurin gaske. Sannan kuma kai mutum mai tausayi da tsoron Allah. Waɗannan suna dalilan da ya sa na ga ya cancanta ka kaji shugaban ƙasa idan wa’adin mulkin sa ya cika.

Da yake jawabi a fadar mai martaba, mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari ya bashi damar ya lelleka kusan ko ina a fanni mulkin kasar nan.

” Hakan ya sa na samu kwarewa matuka wanda zan iya kawo ci gaba a kasar nan, ba tare da an samu wani miskila ba.

Ƴan takarar shugaban kasa na cigaba da ziyarar jihohi domin ganawa da wakilan jam’iyyun su da kuma neman kuri’a.


Source link

Related Articles

2 Comments

  1. You really make it seem so easy with your presentation but I find this matter to
    be really something that I think I would never understand.

    It seems too complex and extremely broad for me. I am looking
    forward for your next post, I will try to get the hang of it!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news