Labarai

TARABA: Mahara sun saki Dan majalisa Bape bayan an biya kudin fansa

Wasu ‘yan uwan dan majalilan dake wakiltar Ngoruje a majalisar jihar Taraba sun bayyana cewa mahara sun saki dan majalisar bayan an biya makudan kudin fansa.

Saidai ba su bayyana ko nawa ne aka biya maharan ba.

Sun kara da cewa tuni har an garzaya da Honarabul Bashir Bape asibiti domin a duba lafiyarsa.

Idan ba a manta ba a cikin wannan mako ne PREMIUM TIMES HAUSA ta buga yadda wasu mahara dauke bindigogi suka yi garkuwa da Bashir Bape.

Honorabul Bashir Bapedake ne yake wakiltar Nguroje a majalisar jihar.

Maharan sun yi garkuwa da Bape a gidansa dake garin Jalingo da misalin karfe daya na daren Talata.

“Maharan sun fatattaki masu gadin gidan bayan dan bata kashi da suka yi kafinnan suka samu damar kutsawa cikin dakin Bape suka yi waon gaba da shi.

Wasu makwabtan Bape sun shaida cewa masu garkuwan sun diro gidan Bape a kan babura.

Idan ba a manta ba ko a ranar 30 ga Disamba na 2017, an taba yin garkuwa da wani dan majalisar jihar sai dai kuma Allah bai sa zai tsira da rai ba, domin sai da aka biya kudin fansa sannan suka kashe shi suka aiko da gawar sa.


Source link

Related Articles

95 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button