Ciwon Lafiya

TARIN FUKA: Ci gaba da wayar da kan mutane zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar – kwararru

Kwararrun jami’an lafiya sun yi kira ga gwamnati da ta ci gaba da wayar da kan mutane game da cutar tarin fuka domin dakile yaduwar cutar a kasar nan.

Shugaban taron ranar tarin fuka ta duniya da aka yi a Abuja ranar Laraba Ayodele Awe ya ce tarin fuka cuta ce da ake warkewa idan an gano cutar da wuri.

“Duk taron ranar tarin fuka na duniya da muke yi kokarin mu shine wayar da kan mutane game da cutar musamman alamun cutar da hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar.

“Yin haka zai taimaka wajen kawar da nuna wa mutane dake dauke da cutar wariya.

Bincike ya nuna cewa Najeriya na cikin kasashe 30 a duniya da tarin fuka ya yi wa tsanani.

Sannan Najeriya ita ce ƙasa ta farko a Nahiyar Afrika dake da yawan mutanen dake dauke da cutar ba tare da sun sani ba.

Duk shekara tarin fuka na yin ajalin mutum 245,000 na a Najeriya.

Mutum 590,000 na kamuwa da cutar duk shekara a Najeriya Mutum 140,000 daga cikin su na dauke da kanjamau.

Mahimmancin wayar da kan mutane game da cutar tarin fuka

Awe ya ce idan mutum na fama da tari fiye da sati biyu kamata yayi ya je asibiti’ domin yin gwajin cutar.

Ya ce yin gwajin cutar kyauta ne a asibitocin kasar nan.

“Kamata ya yi mutane su sani cewa za su iya zuwa kowani asibiti domin yin gwaji da karban maganin tarin fuka kyauta a kasar nan.

Shugaban Hukumar dakile yaduwar tarin fuka da cutar kuturta ta ƙasa (NTLCP) Chukwuma Anyaike ya ce wayar da kan mutane musamman mazauna karkara kan cutar na da matukar muhimmanci.

Anyaike ya ce bullowar cutar korona ya hana samar wa masu fama da cutar kulan da suke bukata.

“Bullowar korona ya hana mutanen dake dauke da cutar zuwa asibiti inda da dama daga cikin su na gida ne a zaune.

“Yana da mahimmanci mutane su sani cewa tarin fuka cuta ce da ake warkewa Kamar sauran cututtuka.

Anyaike ya ce idan har dai mutane sun san haka dakile yaduwar cutar zai zo da sauki a kasar nan.

Ya yi kira ga jami’an lafiya da su Samar wa mutanen da suka yadda suka kawo kansu yin gwajin cutar kula sannan su guji nuna wa mutane irin haka wariya.


Source link

Related Articles

71 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button