Ciwon Lafiya

TARIN FUKA: Yadda cutar ke cigaba da yaduwa a Najeriya saboda sakacin mahukunta

Sakamakon binciken da hukumar gudanar da bincike kan kwayoyin cutar ‘virus’ ta Najeriya IHVN ya nuna cewa jihar Legas ce jihar da ta fi yawan mutanen dake fama da tarin fuka a kasar nan.

Sakamakon binciken ya kuma nuna cewa duk shekara akwai mutum sama da 300,000 dake dauke da cutar ba tare da gwamnati ta san da zaman su ba.

Shugaban shirye-shirye kan yaduwar tarin fuka na asusun USAID ‘TB LON 3’ Olugbenga Daniel ya sanar da haka da yake tattaunawa da manema labarai ranar Talata.

Daniel ya ce rashin gano wadanda ke fama da cutar ka iya kawo koma baya a nasarorin yaki da cutar da aka samu.

Bincike ya nuna cewa a shekara mai dauke da cutar tarin fuka na iya har an mutum 15 a shekara.

Tarin fuka a Najeriya

Tarin fuka cuta ce dake kama huhu mutum inda kwayoyin cutar na Mycobacterium tuberculosis ke hadassa cutar a jikin mutum.

Sakamakon bincike ya nuna cewa Najeriya na cikin kasashe 30 da cutar ta yi wa katutu a duniya sannan na daya a jerin kasashen Afrika da suka fi samun mutanen dake da cutar ba tare da gwamnati ta san da zaman su ba.

Yin allurar rigakafi na cikin hanyoyin samar da kariya daga kamuwa da cutar amma wani sakamakon bincike da kungiyar lafiya ta duniya WHO ta gudanar ya nuna cewa cutar na kisan mutum 245,000 sannan wasu mutum 590,000 na kamuwa da cutar a shekara a duniya.

Sannan daga cikin mutum 590,000 dake kamuwa da cutar mutum 140,000 na dauke da cutar kanjamau.

Bayan haka sakamakon binciken da kungiyar mai zaman kanta ta gabatar a watan Maris 2020 ya nuna cewa an samu koma baya a yi wa mutane gwajin cutar da bai wa masu fama da cutar magani a dalilin bullowar cutar korona.

“Bullowar cutar korona na daga cikin dalilan da ya sa duk shekara ake samu mutum sama da 300,000 dake dauke da cutar ba tare da gwamnati ta san da zaman su ba.

Daniel ya ce ya zama dole a mike tsaye domin dakile yaduwar cutar a kasar nan.

Shirin TB LON 3

Shirin TB LON 3 shiri ne da asusun USAID ta tsaro domin dakile yaduwar tarin fuka a Najeriya.

Babban burin shirin shine gano mutanen dake dauke da cutar da gwamnati ta ƙasa ganowa domin basu magani.

Shirin zai fara aiki daga shekaran 2020 zuwa 2025 a jihohin Lagos, Osun, Ogun da Oyo.

Zuwa yanzu Shirin ta gano mutum 11,000 dake dauke da cutar a kasar nan shirin na sa ran gano mutum 432,000 dake dauke da cutar duk shekara.

Daga shekaran 2019 zuwa 2020 shiri ta samu karuwa a yawan mutanen da take ganowa da cutar daga 120,000 zuwa 130,000.

Wannan nasara na da nassaba da hadin hannun asibitocin gwamnati da wadanda ke zaman kansu.

Matsalar rashin ware isassun kudade

Daniel ya koka da yadda gwamnati take yawan dogaro da tallafin da take samu daga kasashen waje a maimakon ware isassun kudade domin yaki da cutar.

Ya ce yin hakan da gwamnati ke yi na hana a jawo hankalin mutane domin yaki da cutar.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button