Nishadi

TATTAUNAWA: Budurwar gefe na dauke wa namiji tunane-tunane. Lalacewa ne mai aure ya ajiye budurwar gefe

Wakiliyar PREMIUM TIMES HAUSA ta tattauna da wasu mazajen aure a unguwar Kwangila dake Zariya jihar Kaduna kan dalilan da ya za mazajen aure ke neman mata ko suke ajiye farka a waje.

A tattaunawar da ta yi da wadannan magidanta wakiliyar ta jiyo ra’ayoyin wasu mazajen aure suka bayyana cewa bai kamata a ce namiji mai aure ya rika ajiye farka a gefe ba bayan matar sa na gida. Wasu kuma sun ce bariki ce kawai wasu mazajen ba za su iya rayuwa babu wata a gefe da suke tare ba.

Wani Jibirin Hassan wanda aka fi sani da Ustaz dake siyar da doya a ‘Sokale’ ko Kuma ‘Yan goro’ dake Kwangila ya ce tun da addininsa musulunci ya bashi damar ya auri mata 4 idan yana da halin ciyar da su bai ga dalilin da zai sa ya ajiye wata a waje ba tana lashe mishi kudi haka kawai ba.

“Mazan dake ajiye farka Ina ganin kasadan da suke yi domin duk inda aka je basu da gaskiya sun ci amanar matayen su da ke gida.

Shi kuwa Hamisu bakanake ya ce bashi da matsala da ajiye farka matsalar sa shine yadda ajiye su ke da tsadar gaske, yana lashe masa kudi.

“Kin san cewa komai yanzu ya kara tsada sannan dan kudin aikin da kake samu bashi da yawan da har za ka kula da iyalan ka sannan kuma har kasamu wanda zaka kashe wa budurwar ka ta bayan fage.

Jamilu Balarabe ya ce samun farka ga namijin aure na da matukar mahimmanci domin su ne ke taimakawa namiji wajen guje wa wasu matsalolin dake tasowa daga bangaren iyali.

“A gani na farka mace ce dake taimakawa matan aure wajen kula da mazajen su idan sun gaza musmman a lokutan da ita macen baza ta iya ba.

“Idan ka yi dacen budurwar arziki za ki iya zama ga-gida-ga-gida da iyalinka, wasu ma har kyauta za su na rika yi wa ya’yan ka da iyalan ka.

Umar Musa malamin jami’a ya ce ajiye farka ba shi da amfani domin yana daga cikin matsalolin dake kashe aure Kuma yake sa wasu mazan ke ta wahala a rayuwar su.

“La’anar ajiye farka kan shafi ‘ya’ya inda za ka ga yara sun zama yu-yu-yu mutanen banza. Allah ka shirya mana zuri’a amin.

A takaice dai Kwangila wuri ne da magaidanta da dama ke ajiye farka sannan ra’ayinsu shine “Kwangila bariki ne kuma duk tsuntsu da ya ja ruwa shi ruwan kan duka.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button