Labarai

TINUBU/SHETTIMA: Fastocin ƙarya ne suka halarci taron Ƙaddamar da Shettima – Inji CAN

Ƙungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, ta bayyana cewa duka Fastocin da aka gani sun halarci taron kaddamar Kashim Shettima da aka yi a hedkwatar jam’iyyar APC a Abuja ranar Laraba.

Kakakin kungiyar CAN, Bayo Oladeji ya bayyana cewa duk waɗanda aka gani a wurin taron sanye da dogayen rigunan fastoci a wannan wuri duk ba fastocin kwarai bane, na boge ne.

A yau Laraba ne aka ƙaddamar tsohon gwamnan jihar Barno Kashim Shettima mataimakin ɗan takarar shugaban kasa na Ac Bola Tinubu.

A wurin taron an ga wasu da dama sanye da kayan limamen coci-coci a wurin.

Hakan ya jawo cecekuce a musamman kafafen yaɗa labarai na yanar gizo inda wasu da dama ke tsine wa waɗannan fastoci, wasu kuma suna karyata cewa ba fastoci bane kayan ne suka siya a kasuwa suka sassaka domin su nuna kiristoci na tare da Tinubu.

Oladeji ya ce ” Waɗannan fastoci, fastocin karya ne. Kaua ne suka sassaka domin a yaudari jama’a. Abu da yadi ne za a siya akai wa tela ya ɗinka. Amma mu dai kiristoci bamu tare da tafiyar Tinubu da ya zaɓi musulmi mataimaki.

” Mu fa Kiristocin Najeriya bamu tare da zaɓin musulmi da Tinubu yayi har abada, domin cin fuska ne da rainin wayau ma ace wai mun bi irin wannan tafiya na shugaba musulmi, mataimakin shugaba musulmi.

Zaɓin Shettima ya daɗa rura wutar kiyayyarce kawai.


Source link

Related Articles

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button