Nishadi

Tir da waƙar da aka yi wa gogarman ƴan bindiga Bello Turji

Ƴan Najeriya musamman mutanen ƴan kin Arewa sun yi tofin Allah-Tsine wa wanda ya rangaɗawa gogarman ƴan bindiga Bello Turji waƙa na kozarta shi da wasa shi.

A cikin wannan mako wani mawaki, Adamu Ayuba ya saki waka na kozarta gogarmannƴan bindiga Bello Turji wanda a cikin wakar ya rika yabon sa ya na baran yayi masa ƙyautar babur.

A cikin waƙar, Ayuba ya rika jinjina wa Turji da yi masa kirarin ya namijin duniya wanda ya gagari dakarun Najeriya.

Wani mazaunin Kaduna, Sani Bello, ya bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES HAUSA cewa tun da ya saurari waƙar hankalin sa tashi, ” Zuciyata kamar zata fashe saboda fushi.

” Na kasa barci saboda takaici, zuciya ta kamar za ta fashe saboda bakinciki. Ace wai har akwai wani ɗan Arewa da har zai yi wa irin waɗannan mutane waka ana rawa, wannan wani rin lalacewa ne?

Malama Hafsat mazauniyar garin Funtua cewa ta yi, a lokacin da ta saurari waƙar, fashewa da kuka ta yi ta ce ” Na rika sallallami ina kalmar shahada. Lalacewar ta kai lalacewa ace wai mutumin da ya ke gallaza wa ƴan wanka azaba amma kuma kai shine yake burgeka. Wannan wani irin azal ce ta fado mana a Arewa?

Bello Turji ya shahara wanda yanzu shine ake wa ganin shugaban mahara da ƴan bindigan dake dazukan yankin Arewa.

An bayyana cewa yana can yankin Sokoto yanzu tare da gungun mutanen sa suna gallaza wa talakawa azaba.


Source link

Related Articles

95 Comments

  1. 221639 398301Thank you for the auspicious writeup. It in reality was a amusement account it. Look complicated to far delivered agreeable from you! Nonetheless, how can we maintain in touch? 817594

  2. 882096 582335Hi. Cool write-up. There is actually a issue with the internet site in firefox, and you may want to test this The browser will be the marketplace leader and a huge portion of folks will miss your superb writing due to this dilemma. 578703

  3. Pingback: 1untimely

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news