Ciwon Lafiya

TSAKA MAI WUYA: Korona na ƙara kisa, jama’a na ƙaryata cutar, kwalara na kisa, likitoci na yajin aiki

A ranar Asabar da dare ne Hukumar Daƙile Cutar Korona (NCDC) ta buga a shafin ta na Facebook cewa korona ta kashe mutum takwas kuma ta kama mutum 665 a Najeriya.

Wannan fa ƙididdiga ce kawai ta gwajin da asibitoci ko cibiyoyin gwajin korona su ka gabatar. Hakan ya na nufin ba a ma san iyakar waɗanda su ka mutu ko waɗanda su ka kamu ba, waɗanda ba su kai kan su an yi masu gwajin ba.

Daga farkon ɓarkewar wannan cuta zuwa yanzu, ta kashe mutum 2,219 a Najeriya, kuma mutum 181,962 sun kamu. Iyakar waɗanda jami’an kiwon lafiya su ka gwada kenan. Ba a san yawan masu ɗauke da cutar, waɗanda ba su je an gwada su ba.

NCDC ta ƙara da cewa a yanzu haka a Najeriya akwai mutum 12,912 da ke kwance su na jiyyar cutar korona a jikin su. Mafi yawan su kuma a asibitocin kula da masu ciwon su ke kwance, wasu kuma a gida su ke a killlace ana kula da su.

Wannan lamari na sake fantsamar cutar korona ta uku, wato Delta ya zo da ƙarfi, ta yadda a kullum ake samun fiye da mutum 500 da su ka kamu da cutar.

Haka ma a batun mace-mace, ana samun rasa rayukan aƙalla mutum 5 zuwa sama na mutuwa.

A cikin wannan hali ne kuma akasarin ‘yan Najeriya ba su ma yarda akwai cutar ba har yanzu. Yayin da wasu ke haƙiƙicewa su na ƙaryata cutar, wasu da dama kuma na ganin ba daidai ba ne da ake kulle waɗansu wuraren cinkoson jama’a a bar wasu a buɗe. Kulle masallatai a coci-coci ya baƙanta wa da dama na ba’arin jama’a rai.

Hana zuwa aikin Hajji a lokacin da ake wasan Olemfik a Japan, ya sa wasu da dama na ganin kamar lamarin akwai maƙarƙashiya.

In da matsalar rashin yarda da cutar korona ta fi tasiri, yawanci irin al’ummar nan ce da ba su cika yarda akwai wata matsala ba, har sai ta faru a kan su ko kuma a gidan su ko wani na su ko a cikin gidan su.

Yayin da Gwamnatin Tarayya ta nuna cewa ba za ta yi saurin ƙaƙaba dokar kullen-korona ba.

To sai dai a daidai lokacin ne kuma Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ke ci gaba da yajin aikin da babu ranar komawa duba marasa lafiya.

NARD ta ce babu ranar komawa dai Gwamnatin Tarayya ta biya likitoci haƙƙin su. Kamar yadda ita ma Gwamnantin Tarayya ta ce ba za ta biya kowa albashi ba idan bai daina yajin aiki ba.

Cikin wannan mawuyacin hali ne kuma anobar amai da gudawa ko kuma kwalara ta ɓarke a cikin ƙasar nan. Ta kashe ɗarruwan jama’a a jihohin Arewa maso Yamma da su ka haɗa da Jigawa, Kano, Katsina, Zamfara, Sokoto da Kebbi.

Shin ina mu ka dosa ne? Yayin da a kullum ɗaruruwan ‘yan Najeriya ke kwanciyar rashin lafiya daban-daban, babu sahihin adadin waɗanda ke mutuwa, duk kuwa da ƙoƙarin da aka yi aka ce a kullum zazzaɓin cizon sauro na kashe mutum 8 Najeriya.

Ya kamata kowa ya tashi tsaye, a yi ƙoƙarin kare wannan rubdugun dukan da curuttaka ke yi a ƙasar nan, tun kafin dukan ya yi yawa, lokacin da ko na ka ɗin ma a kasa karewa.

Babban laifin gwamnati a wannan mawuyacin hali, shi ne rashin maida hankali wajen tilasta tsaftace muhalli da kulawa a sauran fannonin kiwon lafiya kamar yadda ta ke tayar da hankali, ko ta ke kashe maƙudan kuɗaɗe wajen yayata batun korona.

Babu yadda za a yi talakawan Najeriya su goyi bayan gwamnati wajen ƙin biya wa likitocin da ke sayar da rayukan su a asibitoci. Domin a duk lokacin da gwamanti ta yi kukan rashin kuɗi, shi kuma talaka ya na kallon irin yadda ake kashe mahaukatan kuɗaɗe a lokacin zaɓe.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button