Wasanni

TSANANIN BASHI DA KARAYAR ARZIKI: Akwai yiwuwar a wayi gari babu kungiyar kwallon kafa ta Barcelona

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona sananniyar kungiyace da da ta yi fice wajen siyan fitattun yan kwallo da kuma cin kofi.

Sai dai kuma a dan shekarun da suka wuce cin kofi kamar yadda ta saba ya na neman ya gagareta.

Magoya bayan kungiyar kwallon kafar suna na hannu rabbana suna jiran suga yadda Allah zai yi da kulub din.

Da farko dai tsananin bashi ne ya yi wa ƙungiya katutu ta yadda bata san yadda zata samu kudin biya ba.

Sannan kuma ya kai ga hatta albashi na wannan watar ya gagari kungiyar biyan ƴan wasa. Gaba dayan su sai dai rokon su aka yi su yi hakuri.

Baya ga rashin kudi da basuka da suka yi wa kungiyar katutu, wasu daga cikin ƴan wasan da ƙungiyar ke ji da su dole ta rabu da su ko kuma kwatakwata ya zamanto sai dai su rika yi mata wasa kyauta idan har kungiyar kwallon kafar za ta ci gaba da zama cikin jerin kungiyoyin kwallon kafa na duniya.

A karshen kakakar wasannin kwallon kafa ta bara, shahararren dan wasan kungiyar Leo Messi ya nemi kungiyar ta hakura da shi ya koma wata kulob din amma ta ki.

Ga shi yanzu ya zame mata kaya domin kuwa bata iya biyan sa albashin Dala 500,000 duk wata.

Baya ga haka kungiyar na kokarin ta dawo da tsohon ɗan wasan ta, Neymar daga PSG, da kuma siyan Halaand, wanda hakan yanzu duk sun zama tarihi domin ba ta tasu ake ba domin yanzu ƴan wasan da take ji dasu za ta saida domin ta samu kudi ko kungiyar ta rage zafi.

Ƴan wasa kamar su Dembele, da Griezman da Coutinho wanda dukkan su kamar hasara ne siyan su da kungiyar ta yi duk na daga ciki wadanda za a iya saida wa, saida kuma a yanayin da suka taka leda, ba za su sama mata kudin kirki ba kida an saida su

Jaruman da suka rage ake fafatawa da su kamar su De Jong, Messi, da Ansu Fati ma babu tabbacin za su ci gaba da buga kwallo a Barcelona a irin wannan cakwakiya da kungiyar ta fada.

Wasu kamfanonin dake bin Barcelona bashin maƙudan kudade sun fara ɗaga wa kungiyar kwallon kafan kafa, suna kara mata lokaci domin matsalar rashin kuɗi da take fama fa shi.

A yanzu haka kusan yafe musu albashi Messi ya ke yi saboda matsalar da kungiyar ta shiga.

Magoya bayan kungiyar suna nan sun yi zugum sun zuba wa ikon Allah Ido, ko kungiyar ta farfaɗo ku kuma shi kenan Barcelona ta kare.

Wannan sharhi ne daga shafin Goal.com Premium Times Hausa ta yi muku tsakure daga ciki.


Source link

Related Articles

1,221 Comments