Labarai

TSANANIN RASHIN TSARO A ZAMFARA: Gwamnonin yankin Arewa ba su ba ni haɗin kai ba – Matawalle

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya yi korafin cewa gwamnonin yankin Arewa Maso Yamma ba su bashi haɗin kai wajen ƙoƙarin sulhu da ya ke yi da ƴan bindiga a yankin ba.

” Maimakon gwamnonin yankin su amince da zaɓin a yi sulhu da ƴan bindiga sun ƙi, shi ya sa hare-haren ya yi tsananin gaske yanzu, saboda ba su mara min baya ba.

Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara, ya roƙi Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaƙaba dokar-ta-ɓaci a kan matsalar tsaro, domin a cewar sa, hakan ne kaɗai zai iya magance taɓarɓarewar da tsaro ya yi.

Da ya ke buga misali da jihar sa Zamfara a lokacin da Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Shiyyar Kebbi, Sokoto da Zamfara, AIG Ali Janga ya kai masa ziyara, Matawalle ya bayyana cewa kafa dokar-ta-ɓaci a fannin tsaro ne kaɗai zaɓin da ya rage, domin a magance matsalar.

Ya ce a kullum Zamfara na cikin hare-hare, ta yadda lamarin ya yi ƙazancewar da in ba dokar-ta-ɓaci aka kafa ba, to ba za a iya shawo kan matsalolin ba.

“Ba wanda zai iya bugun ƙirji ya ce ya tsira, ko ya tsallake matsalar tsaron nan. Saboda haka a kafa dokar-ta-ɓaci kan sha’anin tsaro kawai.”

Matawalle ya yi wa AIG Janga wannan bayani ne a cikin wata sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai Zailani Baffa ya fitar a Gusau, babban birnin jihar Zamfara a ranar Laraba.

AIG ya samu rakiyar Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, a ziyarar da su ka kai wa Gwmana Matawalle.

A wani jawabi da Matawalle ya yi aka watsa a jihar, ya zargi ‘yan siyasa da yi wa shirin sa na zaman sulhu da ‘yan bindiga domin a samu zaman lafiya a jihar.

Ya ce lamarin tsaron Zamfara ya sha bambam da na sauran jihohi.

Matawalle ya kuma zargi wasu gwamnoni na Arewa maso Yamma da ƙin yin sulhu da ‘yan bindiga, lamarin da ya ce ya ƙara gurgunta duk wani ƙoƙarin da ya yi na samar da zaman lafiya a Zamfara.

AIG Janga da Kwamishinan ‘Yan Sanda Ayuba Elkhana sun jinjina wa Gwamna Matawalle, wajen ƙoƙarin da ya ke yi na bayar da goyon baya ga ‘yan sandan jihar domin samun zaman lafiya.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button