Nishadi

Tsananin rashin tsaro da wahalar man fetur ya sa haɗin girka shinkafa dafaduka ya yi tsadar gaske

Sakamakon binciken da SB Morgen ya gudanar ya nuna cewa farashin haɗin dafa shinkafa dafaduka wanda zai isa mutum biyar ya tashi daga Naira 8,007 a karshen shekarar 2021 zuwa Naira 8,595 a farkon shekarar 2022 a Najeriya.

Binciken ya nuna cewa Karin kashi 7.3% din da aka samu na da nasaba ne da yadda Najeriya ke fama da karancin man fetur da hare-haren ‘yan bindiga.

SB Morgen ya yi amfani da shinkafa dafaduka domin nuna yadda farashin abinci ke kara hauhawa a kasar nan.

A dalilin wannan bincike SB Morgen ya ziyarci kasuwanin dake kowace bangare a kasar nan inda yaji cewa mutane sun fi rashin jin daɗin tsadar farashin naman talo-talo, naman sa da naman kaza.

Kasuwanin dake Arewa ta Tsakiya mutane sun fi fama da tsadar farashin naman talo-talo, albasa da naman sa.

Binciken ya nuna cewa a yankin naman talo-talo, albasa da naman sa farashin su ya fara hauhawa ne a watan Fabrairu zuwa Maris kuma hakan na da nasaba da yadda ake fama da karancin man fetur.

A dalilin tsada da karancin man fetur direbobin dake safara da jigilar hadahadar kayan abinci sun kara farashin kudin da suke karba saboda yadda suke wahala kafin su samun man da za su zuba a motocin su.

Sakamakon wannan bincike ya nuna cewa tsadar farashin abinci ya fara hauhawa daga shekaru biyar da suka wuce a Najeriya.

Tsadar farashin abinci a Najeriya

Binciken ya nuna cewa matsalolin da suka hada da hare-haren’yan bindiga, rashin ingantacen wurin ajiyan kayan abinci da yawan haihuwan da ake yi a Najeriya sun Isa su sa farashin kudin shigo da abinci daga kasashen waje yayali tashin hwauron zabi.


Source link

Related Articles

2 Comments

  1. Attractive section of content. I just stumbled upon your site and in accession capital to assert that I acquire in fact enjoyed account your blog posts. Anyway I will be subscribing to your feeds and even I achievement you access consistently rapidly.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news