Labarai

Tsarin shugabanci a wurin Tinubu baiwa ce – Inji Osinbajo

Mataimakain Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, ya bayyana cewa irin tsarin shugabanci da jagrancin da Tinubu ya ke da shi, abin jinjina ne matuka, domin ba kasafai ake samun mutane masu irin kokari da baiwar rike jama’a irin Tinubu ba.

Osinbajo ya yi wannan wannan bayani a taron taya Tinubu murnar cikar sa shekaru 69 da haihuwa, wanda aka gudanar a Kano.

Mataimakin Shugaban Kasa dai ya yi magana ne daga gida, kamar yadda masu jawabai da dama duk daga gida su ka yi magana ana kallon su kai-tsaye.

Osinbajo ya ce Tinubu kankin kan sa wata cibiya ce guda ta musamman wadda ta cancanta a yi wa kasaitaccen biki.

“Babu wani shugaba a fadin Najeriya wanda ya cicciba wasu shugabannin su ka hau saman shugabanci kamar Bola Tinubu. Ya yi wannan gagarimin aikin ne saboda ya na da halayen shugabanni nagari.

Ya kara da cewa a koda yaushe Tinubu ya na fadada tunanin sa, kuma ba ya tsoron na kasa da shi su rika tambihin akidoji da ra’ayin sa.

“Babu ruwan sa da kabilanci ko addinanci. Shi kowa na sa ne.” Inji mataimakin shugaban kasa, Osingbajo.

Mataimakin na Buhari ya kara da cewa taron taya Tinubu murna ya zo a daidai, musamnnan saboda an tattauna a daidai lokacin da annobar korona ta yi wa duniya mummunar illa, ba wa ma Najeriya kadai ba.

Daga nan sai ya bayyana wadanda su ka yi taron cewa Najeriya na bukatar wani grup na maza da na mata daga kowane bangaren addini da bangaren kabilanci ko yare, wadanda su ka shirya sadaukar da kansu wajen shugabantar kasar nan da daraja sosai.

Shi kuwa Gwamna Umar Ganduje na Kano, wanda ya jagoranci taron wadanda su ka halarta ido-da-ido ba daga gida ba, ya bayyana cewa zaben da Tinubu ya yi wa Kano, har aka shirya kasaitaccen taron sa a birnin, abu ne mai matukar kyau kuma ya yi wa Kano da gwamnatin Kano dadi sosai.

“Kabilanci, addinanci, bangaranci, kullatar juna da rashin aminta da juna su ne ke kara dankwafar da kasaar nan a baya.” Inji Ganduje.


Source link

Related Articles

81 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button