Labarai

TSIRAICI: Ƴan sanda sun fara binciken tambaɗar fitsara da wata ƴar makarantar Chrisland da abokanta suka yi

Rundunar ƴan sandan jihar Legas sun fara gudanar da binciken bidiyon wata ƴan makarantar attajirai dake Legas, da aka nuno ta tsirara haihuwar uwa akan wani matashin yaro mai shekari 13 suna lalata a dakin Otel a Dubai. Kamar yadda Punch ta buga.

Kakakin yan sandan jihar Legas Benjamin Hundeyin ya ce ƴan sanda sun fara bincike akai kuma za su tabbata sun bankaɗo abinda ya ya auku a cikin wannan bidiyo.

Kafin nan gwamnatin jihar Legas ta sanar da rufe wannan makaranta har sai an gama bincike akai sannan ta gargaɗi mutane da ke da mallakin wannan bidiyo da kada su rika yada shi. Idan aka kama wani yayi haka za a maka shi kotu.

Jaridar Punch ta buga cewa daliban sun tafi kasar Dubai ne domin halartar gasa na makarantu. A wajen kwanan da aka kama wa ɗaliban suka rika yin wasan batsa da yakao da wannan yarin ya ta aikata wannan fitsara tare da abokan ta ɗalibai maza

Sai dai kuma an ruwaito cewa mahaifiyar yarinyar tace an ɗirka wa ƴarta kwaya ne a abu ta sha aka yi lalata da ita da karfin tsiya.

Yan sanda sun ce koma dai menene aka yi za bi baasin abin sauda kafa har sai an gano ainihin abinda kayi, a ina aka yi da sauransu.


Source link

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news