KannyWood

Tsohon Jarumi Samanja Ya Samu Tallafin Naira Miliyan Biyu Daga Sojin Nijeriya

Tsohon dan wasan kwaikwayon nan, Alhaji Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da ‘Samanja Mazan Fama, da ke fama da rashin lafiya, ya samu tallafin kudi Naira Miliyan Biyu daga Rundunar Sojojin Nijeriya.

Babban Hafsan Hafsoshin Sojan Nijeriya (COAS), Manjo-Janar Faruk Yahaya, ya ba da agajin kudi aka kai masa har gida.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa an kai wa Samanja tallafin ne a gidansa da ke Kaduna a ranar Litinin.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa wakilin Babban Hafsan Askarawan, Birgediya-Janar Bitalis Okoro, wato Babban Kwamandan Runduna ta Daya ta Sojojin Nijeriya da ke Kaduna (GOC 1 Dibision), shi ne ya kai wa dan wasan kudin har gida.

A jawabin da ya aika, Janar Yahaya ya bayyana cewa an sanar da shi halin rashin lafiya da Samanja ya ke ciki, wanda hakan ne ya sa ya ga ya kamata ya taimaka masa.

Ya ce rundunar Sojan Nijeriya na alfahari da kusanta kan ta da fitattun ‘yan kasa wadanda su ka yi kyakkyawan tasiri ga al’umma.

A cewar sa, rundunar Sojan Nijeriya ta ji dadin yadda Samanja ya rika inganta kyakkyawan zato game da rayuwar sojoji ga al’ummar Nijeriya ta hanyar wasan kwaikwayon sa, wanda hakan ya rika hasko yadda rayuwa ta ke a cikin barikokin soja.

Karanta kuma Cewar Samanja: Ga ni da rai na, ban mutu ba

Ya ce, “Ta hanyar wannan muhimmiyar rawar da ya taka, ya sama wa kan shi daukaka a fagen harkokin nishadantarwa.

“Baya ga duk abin da Samanja ya yi na hasko kyakkyawan zato game da sojoji, ya kuma kasance abin so ga rundunar Sojan Nijeriya.”

Cikin farin ciki, Samanja ya maida jawabi inda ya tuno da aikin soja da ya taɓa yi.

Haka kuma ya kara karyata ji-ta-ji-tar da aka yada a kafafen soshiyal midiya a makon jiya cewa wai ya rasu.

Bugu da kari, Samanja ya bayyana matukar godiyar sa ga Babban Hafsan askarawan saboda wannan kulawa da ya nuna masa.

Daga nan ya yi kira ga dukkan ‘yan Nijeriya da su zama masu kishin kasa kuma su yi addu’ar ci gaba da samun zaman lafiya da juna a kasar nan.

Haka kuma ya yi kira ga matasa da a ko yaushe su kasance su na samu abin yi wanda zai amfani rayuwar su.

Daya daga cikin ‘ya’yan Samanja, Amina Usman, ta bayyana cewa mahaifin ta mutum ne mai kula tare da kaunar iyalin sa.

Ita ma ta yi godiya ga rundunar Sojan Nijeriya saboda kulawar da ta yi wa iyalan Samanja.

Idan an tuna dai, a ranar Alhamis ta makon jiya an wayi gari da labarin wai Samanja ya kwanta dama.

Wani tsohon darakta a Hukumar Talbijin ta Kasa (NTA) ne ya yi kuskuren rubutawa a shafin sa na Facebook cewa Allah ya yi wa Samanja rasuwa.

Nan da nan labarin ya bazu a soshiyal midiya duk da yakefitaccen dan jaridar nan Ibrahim Sheme ya sanar da wanda ya yi rubutun da kuma jama’a cewa Samanja dai na nan da ran shi.

Sheme da ma’aikacin Hukumar Gidajen Yada Labarai Mallakin Jihar Kaduna (KSMC), wato Shafi’u Magaji Usman, su na aikin rubuta tarihin rayuwar Samanja, don haka sun san bai mutu ba.

Daga baya dai wanda ya fara bada labarin ya dauki gyara, kuma ya goge rubutun nasa tare da bada hakuri.

Don kara dakushe yaduwar da labarin ‘rasuwar’ ke yi a soshiyal midiya, Shafi’u ya yi hirar bidiyo da Samanja a gidan sa da ke unguwar Kabala Costain a Kaduna, kuma aka yada bidiyon, wanda hakan ya taimaka wajen dakili labarin.

A hirar tasu, Alhaji Usman Baba Pategi ya bayyana cewa shi dai ya na nan da ran sa bai mutu ba.

Shi dai Alhaji Pategi, ya fara wasan kwaikwayo tun bayan dawowar sa daga Yakin Basasar Nijeriya, inda ya yi aikin soja, kuma ya ci gaba da gudanar da wasan ‘Samanja Mazan Fama’ da na ‘Duniya Budurwar Wawa’ a gidan Rediyon Tarayya na Kaduna har zuwa lokacin da ya yi ritaya saboda halin manyantaka da kuma rashin isasshiyar lafiya.

Yanzu haka dai akwai yunkurin da wasu ke yi domin su yi masa karin agaji saboda halin da ya ke ciki.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button