Labarai

Tsuguno bata ƙare ba kan wata danbaruwa a mazabar Bali da Gasol na Jahar Taraba

Daga shafin Salihu Tanko Yakasai

A kasidar da Mallam Saadu Zungur ya wallafa kuma daga baya Mallam Aminu Kano ya gyara ta ya kuma karanta ta a taron jam’iyar NEPU a garin Lafia a shekara ta 1953, mai taken SAWABA DECLARATION, ya kunshi abubuwa da dama amma kadan daga cikin su sune:

– A ceto talakawa daga mulkin kama karya na turawan mulkin mallaka da yan koron su, tare da fidda talaka daga cikin talauci.

– Sauya mulkin kama karya na wancan zamanin zuwa mulkin damokuradiya.

– Tabbatar da madafan iko da mulki a karkashin jagorancin talakawa wanda dan su aka yi shi tun farko.

A gani na, wadannan sune ginshikin gwagwarmayar kwato mana yanci a wannan zamani, kamar yadda yake a wancan zamani lokacin da iyayen mu da kakanni su kayi gwagwarmaya suma musamman a Arewa da ma kasar baki daya, a jamhuriya ta daya da ta biyu.

Dan haka, tushen da NEPU ta dasa, wanda jam’iyar PRP a jamhuriya ta biyu ta dora akai, shine ya bamu ikon jajircewa mu tsaya tsayin daka, mu yaki masu mana mulkin kama karya a kasar nan a yau, kuma mu bayyana kin goyon bayan mu ga cin amanar da al’umma suka ba su sanda zuka zabe su, daga sama har kasa, har ma wanda aka nada mukamai.

Jam’iyar PRP ta na nan da ran ta, kuma akidar ta da ka’idojin da suka kafa ta suna ci gaba da ba wa mutane sha’awa, musamman matasa wanda ina cikin su, wanda hakan ta sa nai nazari kuma na yanke shawarar koma wa gida a siyasance domin ci gaba da bada gudunmawa ta wajen ganin an gyara kasar nan.

Babban masifar da ta same mu a siyasance, shine sakin layin akidar SAWABA da muka yi kamar yadda na zaiyana a sama, an chanza wadannan akidojin an maye gurbin su da siyasar yan shan kai, da yan gan-gan, da masu kwadayi, da mayaudara, da yan saida yanci, ga kuma yan jari hujja. Wadannan sune ke jan akalar siyasar mu a zamanin nan. Wannan ce ta sa yau talaka ya rasa yancin sa, kuma hakan ya kara jefa mu cikin wannan yanayi da muke ciki.

Na shiga siyasa shekaru ashirin da biyu da suka wuce da tunanin cewa akida da siyasar yanci sune zasu zama ginshikin siyasar mu, kuma wannan ce ta sa na hada kai da wadanda nake tunanin suma wannan ne tunanin su. Na bi su sau da kafa, bisa ladabi da biyayya. Hakan ta sa nai ta tsalle daga wannan jam’iyar zuwa wata. Na fara da APP wadda ta koma ANPP, sannan muka shiga CPC daga karshe muka kare a APC.

Bayan ficewa ta daga APC, Alhamdulilah zan iya cewa yanzu nima gashin kai na nake ci! Na tsaya da kafa ta, kuma ina da yancin fadar ra’ayi na kai tsaye ba tare da shayi ba. Yanci kuma shine gishirin rayuwa, musamman a siyasance, ba abinda ya kai yanci muhimmanci a siyasan ce.

Na dade ina shaawar jam’iyar PRP saboda akidar ta, da jajircewar ta, duk da matsalolin da suke addabar siyasar wannan zamanin, haka kuma na dade ina shaawar tarihin ta. Ganawa da nayi da wasu daga cikin jagororin ta, ya na daya daga cikin abubuwan da suka sa na yanke shawarar shiga jam’iyar PRP. Bayan adduah, shawarwari, da tuntuba, shi yasa na yanke shawarar shiga jam’iyar PRP Nasara, jam’iyar mu ta gado, ta kaka da kakanni, jam’iyar talakawa!

A wannan gwagwarmayar, hawa katanga ba namu bane, ihu bayan hari ba abin yi bane, sannan mu yi ta suka ba ma shiga ana damawa da mu ba zai kawo mana chanjin da muke raji ba. Dole sai mun tsunduma cikin harkar nan tsundum, sannan zamu iya kawo chanji, mu cika burin magabatan mu na ganin kasar mu ta ci gaba domin kannen mu, da ‘ya’yan mu da jikokin mu har ma da wanda za’a haifa can gaba.

Dan haka nake kira ga yan’uwa na matasa, maza da mata, da su zo mu shiga jam’iyar PRP. Jam’iyar Mallam Balarabe Musa, da Abubakar Rimi, da kuma Mallam Aminu Kano. Wannan jam’iyar Mallam Balarabe Musa ya rike ta tsahon ran sa, inda ya raya ta har ta kawo yanzu bayan rasuwar na gaba da shi. Sannan bayan shi, yanzu aka samu wanda suka ci gaba da jan akalar shugabancin ta, domin raya ta. Dukkan su burin su kenan, jam’iyar nan ta rayu bayan su, ta kuma zo kan mu domin mu ci gaba da raya ta har jikokin mu.

Wannan gwagwarmayar yau ta mu ce, kuma dole mu rungume ta hannu bi-biyu da kauna da kishi, da jajircewa da rashin tsoro. Kuma ina fatan yan’uwa da abokai na zasu shigo ta, domin mu ci gaba da raya ta, mu zamanantar da ita, mu kuma tabbatar ta kafa mulki domin cimma burin wanda suka kafa ta na ganin an gyara kasar nan. Ba mu da wani zabi da ya wuce PRP, ita ce zata bamu damar gyara kasar nan da Izinin Allah.

Da ni, da sauran yan’uwa na daga jihohi daban daban da muka shiga jam’iyar PRP a yau, babban abinda yake gaban mu na farko shine kokarin ganin mun dinke jam’iyar ta zama daya, mu kuma zamanantar da ita domin ya zamanto zata iya gogayya da kowacce jam’iya a Afirka ma ba Najeriya ba, domin samar da gwamnati ingantacciya ta gari, mai kishin al’ummar ta. Dinkakkiyar jam’iyar PRP ina da yakinin zata iya lashe duk wani zabe a kasar nan, musamman ma a Arewa inda nan ne cibiyar ta. Ina godewa wadanda suke rike mana jam’iyar PRP Nasara, bisa namijin kokarin da suka yi. Allah saka musu da alheri amin. Ina kuma kira a gare su da su ba mu hadin kai, mu dunkule domin tabbatar da Nasara. Hanya daya tilo da zamu samu nasara shine ta “ZERO TENSION” tunda dai mun san Allah ne mai yi, kuma muna na mu, Allah na nashi, ba kuma abinda Ya gagari Allah. Dan haka nake ganin lokaci yayi, da zamu farfado da PRP, domin muyi nasara In sha Allah!!!

Nagode Allah tabbatar mana da NASARA! Amin!

Barka da juma’a yan’uwa musulmi.

Salihu Tanko Yakasai (Dawisun Kano)
Sabon dan jam’iyar PRP
Masoyin Kano da Arewa da Najeriya.


Source link

Related Articles

5 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news