Labarai

UMARNIN SALLAMA DA KUJERAR MINISTA: Pauline Tallen, Timiprr Sylva duk sun janye daga takara

Ministan harkokin mata Pauline Tallen da na Harkokin man fetur Timipre Sylva sun janye daga takara a zabukan 2023.

Hakan na kunshe na a sanarwar da ministar ta saka wa hannu wanda aka mika wa manema labarai ranar Litinin a Abuja.

Ta ce ta janye ne domin ta mai da hankali wajen ayyukan ma’aikatar da take shugaban ta wato ma’aikatar ayyukan mata.

Idan ba a manta ba a ranar 8 ga Mayu Pauline ta bayyana cewa za ta fito takarar kujerar sanata na yankin Filato ta kudu.

Akwai kananan hukumomi shida dake karkashin Filato ta Kudu da suka hada Langtang ta Arewa, Langtang ta Kudu, Mikang, Qua’anpan, Shendam da Wase.

Sai dai kuma a ranar Alhamis din da ta gabata shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya umurci duk wani minista ko jami’in gwamnati da ke takarar shugaban Kasa, gwamna ko majalisar jiha da na kasa, ya ajiye aiki nan da ranar 16 ga Mayu.

Zuwa yanzu ministan kimiya da fasaha Ogbonnaya Onu, ministan Neja-Delta Godswill Akpabio da karamin ministan ilimi Chukwuemeka Nwajiuba duk sun ajiye aiki.

Sai dai kum.akwai ministan Shari’a Abubakar Malami wanda shima da ya fito takarar gwamnan Kebbi amma kuma dalilin wannan sanarwa ya janye.

Shima ministan Albarkatun man fetur, Timipre Silva, ya janye daga takarar shugaban kasa da ya fito.

Silva ya ce gwara ta koma ma’aikatan sa ya cigaba da aiki maimakon takarar da ya fito nema.


Source link

Related Articles

7 Comments

  1. We are a group of volunteers and starting a new scheme in our community. Your website offered us with valuable info to work on. You’ve done an impressive job and our entire community will be grateful to you.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button