Ciwon Lafiya

USAID ta tallafawa Najeriya da naurorin yin gwajin Tari fuka 86,500

Kungiyar USAID ta tallafa wa Najeriya da na’urorin yin gwajin cutar tarin fuka mai suna ‘GeneXpert Ultra’ 86,500 domin inganta yaki da cutar a kasar nan.

Na’urar na da ingancin gano kwayoyin cutar a jikin mutum sama da 10,000.

Baya ga haka na’urorar mai suna ‘GeneXpert Ultra’ zai taimaka wajen gano mutanen da cutar baya jin magani a jikin su sannan da gano cutar a jikin mutanen dake fama da cutar kanjamau.

Idan ba a manta ba a watan Janairu, uwargidan gwamnan jihar Legas Ibijoke Sanwo-Olu ta kaddamar da sabbin motoci guda uku na tafi da gidanka da za a rika yi wa mutane gwajin cutar tarin fuka a ko-ina suka a fadin jihar.

Ibijoke ta bayyana cewa motocin za su rika yawo a jihar suna yi wa mutane gwajin cutar nan take da kuma basu magani kyauta.

Bayan haka Ibijoke ta ce gwamnatin jihar ta zuba na’urorin gwajin cutar a wasu zababbun asibitoci 18 dake jihar domin su rika yi wa mutane gwajin cutar da basu magani kyauta.

Bincike ya nuna cewa a shekarar 2019 akwai mutum 38,277 dake fama da cutar ba tare da sanin gwamnati ba a jihar.

Sannan duk shekara cutar na kashe 245,000 kuma wasu 590,000 na kamuwa da cutar a Najeriya.

Idan ba a manta ba asusun bada tallafi na duniya wato Global fund, ya baiwa Najeriya zunzurutun kudi har dala miliyan 500 tare da wasu kasashen Afrika 10 domin yaki da tarin fuka a cikin shekara uku masu zuwa.

Asusun zai kashe dala biliyan 12.7 a kasashe masu tasowa domin yaki da cututtukan kanjamau, tarin fuka da zazzabin cizon sauro.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button