Labarai

Ya kamata ƙabilar Igbo su rungumi Tinubu, su daina nukura da shi – Nnamani, Sanatan PDP

Sanatan PDP daga Jihar Enugu, Chimaroke Nnamani, ya kira ga ƙabilar Igbo arankatakaf cewa su rungumi ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Bola Tinubu domin ya yi nasara a zaɓen 2023.

Cikin wata sanarwar da ya fitar ga kafafen yaɗa labarai, har da PREMIUM TIMES, Nnamani ya ce ya cancanci su zaɓi Tinubu, saboda irin gagarimar rawar da ya taka wa ƙabilar Igbo a rayuwar sa.

Nnamani wanda ɗan PDP ne, amma bai fito ya tallafi takarar Atiku Abubakar ba, ya ce ƙabilar Igbo su daina nukura ko nuna ƙiyayya ga Yarabawa.

Ya fara buga misali da yadda Gwamnan Yankin Yamma na mulkin soja, Adekunle Fajuyi ya sadaukar da ran sa a 1966 wajen kare Shugaban Mulkin Soja na lokacin, Janar Irinsi wanda ‘yan juyin mulki su ka kashe su tare.

Nnamani ya ce Tinubu ya cancanta, don haka ƙabilar Igbo ta bi Tinubu kawai. Batun haƙilon mulkin Najeriya da Igbo ke yi kuwa a yanzu, ya ce su haƙura, su bi Tinubu, sai su sake ƙaƙƙarfan shiri a gaba.

Farkon fara kamfen ɗin Atiku dai sai da Nnamani ya fito ya ce ganganci ne ya sa PDP ta fara kamfen ba tare da gwamnonin ta biyar ba.

Tsohon Gwamnan Jihar Enugu, kuma Sanata a yanzu, Ken Nnamani, ya ce babban kuskure ne da ganganci da har jam’iyyar PDP ta fara kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa, ba tare da gwamnonin jam’iyyar biyar daga kudu ba.

Nnamani ya bayyana haka cikin wata sanarwar da ya aiko wa PREMIUM TIMES a ranar Talata.

Ya ce kwata-kwata ba daidai ba ne, kuma kasada ce babba a ce PDP ta fara yaƙin neman zaɓen ta a kudu, Jihar Akwa Ibom, ba tare da gwamnonin kudu biyar da ke cikin jam’iyyar ba.

Ya ce bai ga yadda za a yi nasara ba, idan gwamnonin biyar su ka ƙi bayar da haɗin kai lokacin zaɓe a jihohin su.

Ya ce ko an ƙi, ko an so gwamnonin jagorori ne a jihar su, kuma su ne kusa da jama’ar karkara ba ‘yan siyasar Abuja ba.

“Shi ɗan siyasar Abuja aikin shi kaɗai ya baza babbar riga ya shirya taron gangami, daga ranar kuma ba a ƙara ganin shi a jihar. Gwamna shi ne mai jama’a. Don haka idan ka wulaƙanta gwamna, to tamkar ka haɗa ne har da na ƙarƙashin sa duk ka wulaƙanta su.”

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Jirgin yaƙin PDP na tangal-talgal, saboda gwamnoni biyar sun ƙi hawa a yi lodin kamfen tare da su.

Duk da cewa jam’iyyar PDP ta ƙaddamar da kamfen ɗin yaƙin neman zaɓen 2023 a Akwa Ibom cikin nasarar tara ɗimbin jama’a, ƙaurace wa gangamin da gwamnoni biyar su ka yi ya nuna har yanzu akwai jan-aiki ga Atiku sosai kafin ya dangana da kujerar shugaban ƙasa.

Gwamnonin guda biyar da ba su halarci taron ba, sun haɗa da Nyesom Wike na Jihar Ribas, Seye Makinde na Jihar Oyo, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu, Ikpeazu Okozie na Abiya sai kuma Samuel Ortom na Jihar Benuwai.

Su huɗun su na goyon bayan Wike ne, wanda ya jagorance su bijire wa PDP bayan an tsayar da Atiku takarar shugaban ƙasa.

Su biyar ɗin dai su na neman tilas sai shugaban PDP, Iyorchia Ayu ya sauka a naɗa ɗan Kudu, domin a tabbatar da adalci a shugabancin PDP.

Gangamin wanda PDP ta yi a Filin Wasa na Godswill Akpabio International Stadium, ya cika fal da magoya bayan PDP, inda a wurin Atiku ya sha alwashin cewa idan aka zaɓe shi, to za a yi bankwana da talauci da matsalar tsaro da rashin aikin yi a Najeriya.

Idan ba a manta ba, waɗannan gwamnoni biyar ba su halarci taron ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na PDP ba.

Masu bibiyar lamarin siyasa na ganin cewa PDP za ta iya fuskantar matsala matsawar ba ta sasanta da gwamnonin biyar ba.

Su Wike dai su na jin haushin yadda ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da kuma Shugaban PDP Iyorchia Ayu duk su ka fito daga yankin Arewa.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da rundunar yaƙin Bola Tinubu na APC ta ce, rikicin da hasalallun gwamnonin PDP ke yi da shugabannin jam’iyyar su, alheri ne ga APC.

Rundunar Yaƙin Tinubu 2023 ta ce turnuƙun rikicin da wasu hasalallun gwamnonin PDP ke yi da shugabannin jam’iyyar su, alheri ne ga jam’iyyar APC.

CIkin wata sanarwa da ɗaya daga cikin Kakakin Yaɗa Labaran Rundunar Tinubu, Festus Keyamo ya fitar a ranar Asabar, ya ce rikicin da ke faruwa a cikin PDP ya nuna cewa jam’iyyar ba za ta iya riƙe mulkin Najeriya ba, tunda har yau ta kasa ma sasanta rikicin da ke cikin gidan ta.

Keyamo ya ce PDP ba za ta iya haɗa kan Najeriya ba, tunda ta kasa haɗa kan iyayen jam’iyyar PDP ɗin.

Hasalallun gwamnonin dai bisa jagorancin Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, har yau sun ƙi goyon bayan takarar shugabancin ƙasa da Atiku Abubakar ke yi, bisa dalilin cewa babu adalci wajen raba muƙaman jam”iyyar, saboda an damƙa shugabancin PDP ga ‘yan Arewa, inda kuma a yankin ne ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya fito.

Gwamnonin dai sun gindaya cewa kafin su fara goyon bayan Atiku, tilas sai Shugaban PDP, Iyorchia Ayu ya sauka an naɗa ɗan Kudu, domin a yi adalci.

Sannan kuma zargin da Wike ya yi wa Ayu kwanan nan, cewa ya raba wa shugabannin jam’iyyar cin hanci, kuma ya karɓi naira biliyan 1 a hannun wani a Legas, ya ƙara jefa PDP cikin ruɗani.

Keyamo ya ce har yau jam’iyyar PDP ba ta tuba daga ɗabi’ar ta na wawurar kuɗaɗe ba. Don haka ba za ta yaudari ‘yan Najeriya ba a zaɓen 2023.

“Ai mu rikicin da wasu gwamnonin PDP ke yi da shugabannin jam’iyyar su, alheri ne a gare mu. Sun kasa haɗa kan su, kuma rikicin wuru-wurun kuɗaɗe ya ƙara dagula PDP. Hakan ya nuna har yau ba su tuba daga ɗabi’ar su ta sata ba.

Keyamo ya ƙara caccakar PDP cewa sun bi son ran Atiku, sun ƙi bai wa Kudu takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, kamar yadda su ka yi yarjejeniya a baya.


Source link

Related Articles

5 Comments

  1. 👉 $5,000 FREE EXCHANGE BONUSES BELOW 📈 👉 PlaseFuture FREE $3,000 BONUS + 0% Maker Fees 📈 + PROMOCODE FOR NEWS USERS OF THE EXCHANGE 👉 [M0345IHZFN] — 0.01 BTC 👉 site: https://buycrypto.in.net Our site is a secure platform that makes it easy to buy, sell, and store cryptocurrency like Bitcoin, Ethereum, and More. We are available in over 30 countries worldwide.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button