Labarai

Yadda ƴan bindiga suka dira garin Tangaza kamar za su garkuwa da mutane ashe abinci suka zo biɗa

Ƴan bindiga masu yawa dauke da manyan makamai sun dira garin Tangaza, karamar hukumar Gidan Madi da ke jihar Sokoto ranar Juma’ a da dare suka suka farfasa shaguna suna ɗibar abinci.

Majiya da dama sun shaida cewa maharan sun ɗauki mintina 40 suna kwasar kayan abinci da duk wani abu na ci da suka gani.

” Muma abin ya bamu mamaki domin sun shigo garin bisa babura suna ta harbe-harbe amma kuma basu harbi kowa ba. Shaguna da gidaje suka shiga suka rika jidar abinci da kayan abinci.

Basu kashe mutum ko ɗaya sannan basu sace kowa ba. Sun dai ɗibi kayan abinci ne suka yi tafiyar su.

Wani Aminu Sodangi da ya iske maharan a garin Tangaza ya kara da cewa ” Lallai maharan ba su ji wa kowa rauni, kisa ko kuma sace wani ba, abinci suka sata. Da alama dai yunwa ce to koro su daga cikin daji suka fito neman abinci karfi da yaji.

Mahara a yankin Arewa Maso Yammacin kasar nan ba su ji da daɗi yazu domin gwamnatin Tarayya ta saka su a gaba ta na ragargazar su. Zama a cikin dazukan ma yanzu yana neman ya gagaresu domin sojoji farautar su suke yi yanzu.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button