Labarai

Yadda Ƴan bindiga suka kashe Ƴan sanda biyu a Ɓaure, jihar Katsina

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa ta rasa ma’aikata biyu a arangamar da ƴan sanda suka yi da ‘yan bindiga a kauyen Baure dake karamar hukumar Safana.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sanusi Buba ya sanar da haka ranar Juma’a a taron da ya yi da manema labarai a hedikwatar rundunar.

Buba yace rundunar ta rasa ASP Yakubu Joshua da sajen Zaharadeen Yuguda a wannan arangama da jami’an tsaro suka yi da ‘yan bindiga.

“Jami’an mu sun yi batakashi da ‘yan bindiga ranar Alhamis a kauyen Baure bayan rundunar ta samu bayanin siri kan maɓoyar maharan a dajin Baure.

“Samun wannan rahoto na sirri sai ACP Aminu Umar ya ɗibi wasu ‘yan sanda da ‘yan banga zuwa dajin Baure.

“Jami’an tsaron sun kashe mutum biyu daga cikin maharan kuma sun fatattaki sauran.

“An kwato bindiga guda daya kirar AK47, harsasai 35, babura guda biyu da basu da rajista da layuka a maɓoyar maharan.

Jihar Katsina na cikin jihohin yankin arewa dake fama da aiyukkan ‘yan bindiga a kasar nan.

Domin kawo karshen aiyukkan maharan gwamnatin jihar ta dauki wasu tsauraran matakai da suka hada da katse layukan sadarwa, hana siyar da man fetur a galan, da rufe kasuwanin mako-mako.

Duk da waɗannan matakai ƴan bindigan basu daina kai wa mutane hari ba a ɓangarorin jihar.


Source link

Related Articles

7 Comments

  1. Hey! Quick question that’s completely off topic. Do you know how to make your site mobile friendly? My blog looks weird when browsing from my apple iphone. I’m trying to find a theme or plugin that might be able to correct this problem. If you have any recommendations, please share. With thanks!

  2. 955924 528295Hey I was just searching at your internet site in Firefox and the image at the top with the link cant show up correctly. Just thought I would let you know. 464842

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news