Labarai

Yadda aka damke ɗaliba da bindigar saurayinta a makarantar sakandare

Wata dalibar makaranta mai shekaru 17 na fuskartar tuhumar ƴan sanda bayan an kama ta da bindiga a makaranta.

Ita dai wannan ɗaliba, ta bayyana wa ƴan sanda cewa bindigan saurayinta ne ta dauko shi zuwa makaranta.

” Babu mai shiga ɗaki nansai saurayi na. Da naga bindigar sai da dauke na kawo ta makaranta.

” Shugaban makarantar, ya bayyana wa jami’an ƴan sanda cewa ko da aka kama wannan daliba da bindiga, ban yi wata-wata ba sai na kira ƴan sanda su zo su karbi bindigar.

Haka kuma shugaban makarantar dake jihar Cross Rivers, ya kara da cewa tuni har ƴan sanda sun yi awon gana da wannan ɗaliba da saurayin ra da ta ce shine mai bindigar.

Daga baya an gano cewa wai an aiketa da bindigar ne ta kai gyran sa a wajen wani makeri.

A karshe shugaban makarantar ya karyata labaran da ake ta yaɗawa wai ta kawo bindigar makaranta ne domin ta bindige wani malaminta da shi


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button