Nishadi

Yadda cefanen haɗa lafiyayyar dafa-duka (Jollof rice) ya ƙaru, aka bar talaka da cin shinkafa garau-garau

Yayin da ake fama da tsadar rayuwa daidai lokacin da kayan abinci da fetur ke ƙara tsada, bincike ya tabbatar da cewa farashin kayan haɗin lafiyayyar dafa-duka (Jollof rice) a Najeriya ya ƙaru sosai. Haɗin dafa-dukar da a kwanan baya ake kashe naira 8,595, yanzu sai an kashe wa iyali naira 9,311 wajen haɗa ta.

Rahoton SB Morgen na Watannin Huɗun Farkon Shekara ya tabbatar da haka.

SB Morgen ya nuna an samu ƙarin kashi 8.3 a binciken da aka yi cikin kasuwannin sayar da kayan cefane 13 a yankunan ƙasar nan daban-daban. Sai dai kuma adadin kuɗin da ake magana za’a kashe, ana magana ne kan abincin iyalin da ba su wuce mutum biyar ba.

Cikin makon jiya ne Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (National Bureau of Statistics), ta ce rayuwa ya ƙaru da kashi 18.60 cikin watan Yuni, tsadar da bai taɓa yin kamar ba daga bana abin da ya kai shekaru biyar baya. Rayuwar ta yi tsada ne saboda dalilai da yawa a kwanan nan, ciki har da tsadar kayan abinci da fetur da gas na girki.

Kayan haɗin Jollof ɗin da aka binciki farashin su sun haɗa da shinkafa, kori, ‘thyme’, man gyaɗa, kaza, naman shanu, gishiri da albasa.

A ranar Talata SB Morgen ya yi binciken da ya nuna cewa farashin kayan cefane ya riƙa ƙaruwa tun daga Janairu har zuwa Yuni.

“Ƙarin farashin ya danganta da matsalar fetur, faɗuwar darajar naira, munin matsalar tsaro, yanayin da duniya ta ke ciki, kamar sakamkon da yakin Rasha da Ukraniya.

“Dalili kenan kafin mai kaya ya kai kaya kasuwa, kuɗaɗen da ake dakon kayan da yi masu hidima ƙaru sosai, shi ya sa su ke ƙara tsada a kasuwa.”

Matsalar tsadar mai ta sa masana’antun da ke kunna janareto su na sarrafa kaya sun ƙara farashi, domin a baya su na sayen dizal Naira 540. Yanzu kuma Naira 800 duk lita ɗaya.

Yayin da a Bauchi gida mai mutum biyar za su kashe Naira 11,600 a Bauchi, a Wuse II Abuja kuma Naira 11,300 ne.

Haɗa lafiyayyar dafa-duka ta gida mai mutum biyar ya fi tsada a Arewacin Najeriya, duk kuwa da cewa an fi samun dabbobi da yawan noma da ake yi a yankin.


Source link

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button