Labarai

Yadda EFCC ta damke Akanta Janar din Najeriya bisa zargin harkallar naira biliyan 80

Hukumar EFCC ta damke Akanta Janar ɗin Najeriya Ahmed Idris a filin jirgin saman Kano zai yi tafiya.

Bayan kama shi jami’an hukumar sun nausa da shi babban birnin tarayya Abuja, Hedikwatar Hukumar.

Wani jami’in hukumar ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa hukumar ta daɗe tana gayyatar Idris ya bayyana a gaban ta bisa zargin harkallar kudade amma ya ki bayyana.

Ana zargin Ahmed Idris da yin harkallar naira biliyan 80 ta hanyar yin aringizo a wasu kwangilolin karya, da sunayen wasu kamfanoni mallakin ƴaƴan sa da ƴan uwa.

” Mun yi ta aika masa da gayyata ya bayyana a ofishin EFCC amma yadda kasan kana yi da dutse bai amsa gayyatar ba.


Source link

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button