Ciwon Lafiya

Yadda gwamnatin Najeriya ta ki maida hankali wajen dakile yaɗuwar ciwon Sikila a ƙasar

Jami’an lafiya sun koka kan yadda gwamnatin Najeriya ke nuna halin-ko-in kula wajen tsara hanyoyin dakile yaduwar ciwon Sikila a kasar nan.

Sakamakon bincike ya nuna cewa ana haifan yara 150,000 da wannan ciwo a Najeriya sannan a duniya 300,000 duk shekara.

Binciken ya kuma nuna cewa ciwon na yin ajalin yara 100,000 daga cikin 150,000 din da ake haifa da ciwon a kasar nan.

Duk da haka babu wani abin a zo a gani da gwamnati ta yi wajen dakile yaduwar cowon ko samar da kula ta musamman ga masu fama da ciwon.

Wakiliyar PREMIUMTIMES ta nemi karin haske game da matakan dakile yaduwar ciwon Sikila da gwamnati ta yi a ma’aikatar lafiya.

Ciwon Sikila

Bisa ga bayanin da MedScape ta bada ya nuna cewa ciwon sikila ciwo ne dake harbin jinin jikin mutum kuma ana iya gadon sa daga wajen iyaye.

Ciwon ya shafi rashin samun isasshen jini wanda ake kira ‘Redbloodcells’ dake daukan iska ‘Oxygen’ zuwa bangarorin jiki.

Ciwon na haddasa matsalolin da suka hada da shanyewar bangaren jiki, ciwon kirji, ciwon kafa, hawan jini, makanta da sauran su.

Jami’an lafiya sun ce rashin samun iska na ‘Oxygen’ a duk bangarorin jiki na cikin matsalolin dake sa masu fama da ciwon suna rika Suma, shanyewar bangaren jiki da sauran su.

Yadda ya kamata a kula da mai dauke da ciwon sikila

Wata likita kuma shugaban gidauniyar ‘Sickle Cell Foundation Nigeria’ Annette Akinsete ta koka kan yadda ba a ba masu dauke da wannna cuta kyakkawar kula.

Annette tace a lokuta da dama likitoci kan yi kuskure wajen bada maganin karin jini wa mutumin dake fama da wannan cuta wanda hakan ke da mummunar hadari.

“Banda maganin rage radadin jiki da ake bai wa masu fama da ciwon kamata ya yi a rika ba shi Folic acid domin shine ke ke taimakawa jini a jiki.

Likitan ta kuma ce ya kamata a bai wa masu cutar sikila maganin kare su daga kamuwa da zazzabin cizon sauro wato ‘prophylaxis’.

Annette ta ce mai dauke da cutar ya rika shan ruwa ko kuma abinci mai ruwa ruwa domin guje wa bushewar jiki.

Abinda bincike ya nuna game da ciwon sikila a Najeriya

Sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta gudanar ya nuna cewa kashi 5% na mutane a duniya na fama da wannan cuta.

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasar Amurka CDC ta bayyana cewa ciwon ya fi yaduwa a kasashen Afrika fiye da ko Ina a duniya.

CDC ta ce daga cikin yara 300,000 din da ake haifa da cutar a duniya Kudu da Saharan Afrika na da kashi 75% sannan Najeriya na da kashi 60%
Jami’an lafiya sun ce yaran da ciwon ya fi yin tsanani a jikinsu na mutuwa kafin su kai shekaru biyar.

WHO ta ce mutum kashi 24% na dauke da cutar a Najeriya sannan ana samun jarirai 20 da aka haifo da cutar daga cikin jarirai 1,000 a kasan.
A kasashen Afrika Kamar su Kamari, Gabon, Ghana, Jamhuriyyar Kongo da Najeriya ana samu kashi 20% zuwa 30% din da ake haihuwa da ciwon sannan kasar Uganda ana samun Yara Kashi 45%.

Duk da haka sakamakon WHO ya nuna cewa Najeriya ta fi yawan samun yaran da ake haihuwa d wannan cuta a Afrika.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button