Nishadi

Yadda Hadiza Gabon ta yaudare ni ta lamushe min kuɗi taki aure na ba yan mun yi alƙawarin haka

Wani ma’aikacin gwamnatin jihar Zamfara, Bala Musa ya maka fitacciyar ‘yar wasan Hausa Kannywood Hadiza Gabon a kotun Shari’a dake jihar Kaduna bisa zargin karya alkawarin aure da suka yi.

Musa ya ce sai da ya kashe ma Gabon naira 396,000 ɗawainiya da ya riƙa yi da ita.

Ya kamata Hadiza da Musa su gabata a kotun sranar Litini amma sai ota ba halarci zaman kotun ba.

A kotun Musa ya ce ya dade yana soyayya da Hadiza , a dalilin haka ne ya sa har suka yi wa juna alƙawarin aure.

“Daga lokacin da muka fara soyayya na kashe mata Naira 396,000. Duk lokacin da ƴan buƙatun sa suka taso ni ne nake biya mata su.

“Hadiza ta ki zuwa wurina a Gusau bayan mun kammala Shirin cewa za ta kawo min ziyara daga nan mu fara shirin aure.

Kotun ta fara shari’a ranar 23 ga Mayu amma a lokacin Hadiza bata a kotun.

Lauyan dake kare Hadiza Mubarak Kabir ya ce Hadiza ba ta zo kotun ba saboda ba ta da tabbacin ko sammacin da kotun ta aiko na gaske ne.

Kabir ya ce bisa ga irin aikin da Hadiza take yi dole ta riƙa taka tsantsan wajen irin mutanen da suke cewa sun santa ko kuma wata alaka ya shiga tsakanin su.

Ya ce kotu ta bashi dan wani lokaci domin ganin Hadiza ta zo kotun a zama na gaba.

Alkalin kotun Rilwanu Kyaudai ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 13 ga Yuni.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button