Wasanni

Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

” Abin bai yi mana daɗi ba. Tun kafin a gama wasan ƴan kallo suka tsunduma cikin filin wasa na Sani Abacha da ake buga wasa. Alƙalin wasa ya tsaida wasan.

Ƴan kallo sun fusata ne don ƴan kwallon Katsina United sun tare gida sun hana Pillars cin wasa.

An tashi wasa babu ci.

Rashin yin nasara da Pillars bata yi ba ya sa ƴan kallo suka diranma Katsina United.

Darektan yaɗa labarai na kungiyar Katsina United ya Sani Gide ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa tun kafin a kammala wasan a cikin fili, matasa suka fito suka farfasa motar.

” Tun ana cikin fili ana buga wasa, wasu suka fito suka farfasa motar, sannan suka shiga cikin motar suka ka yi ɗan hali, wato suka sace kayan ƴan kwallon da ke ciki. babu wani abu da suka bari a cikin motar.

A karshe ya ce an baiwa kungiy kwallon kafan aron mota da zai maida su Katsina.

An yi shekaru ba a yarda wa Pillar ta buga wasan ta nangida a Kano ba saboda irin haka.

Sukan buga wasa ne a Katsina ko a Kaduna a duk lokacin da suka wasan su na gida.

Gaba ɗaya ƴan kwallon da jami’an su sun koma Katsina babu komai nasu da suka zo da su.


Source link

Related Articles

4 Comments

Leave a Reply to Yuonne Goldeman Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news