KannyWood

Yadda mu ka tsallake rijiya da baya

SUBHANALLAH! Fitacciyar mawaƙiyar nan da ke Kaduna, Jamila Muhammad, wadda aka fi sani da Jamila Kogi, ta tsallake rijiya da ƙundun baya ita da wasu abokan sana’ar ta ‘yan garin su a kan hanyar su ta komawa Jihar Kogi daga garin Lafiya a Jihar Nassarawa.

 

Wannan mummunan al’amari ya faru ne a safiyar jiya Juma’a da misalin ƙarfe 11:00, inda motar da su ka shigo ta yi ƙundunbala da su, sanadiyyar wata babbar mota. 

 

Jamila ta yi wa mujallar Fim cikakken bayanin yadda al’amarin ya faru kamar haka:

 

“Assalamu alaikum! Abin da ya faru, mu na bayan wata babbar mota ne, sai wata mota ta taho a guje. 

 

“Shi mai babbar motar ya na ƙoƙarin taka birki, motar kuma idan direban ya ce zai taka birki za mu shige ƙarƙashin wannan babbar motar, sannan kuma ga wasu motoci biyu su ma su na ƙoƙarin kaucewa, mu kuma sai direban mu ya kauce.

 

“Nan ma kaɗan ya rage mu haɗa jiki da waccan motar, kaucewar da ya yi sai motar mu ta juya, mu ka faɗa rami, tayoyin sun koma sama, saman motar na ƙasa. 

 

“Cikin ikon Allah, mu ka samu mu ka fita ta tagar motar.

 

“Babban abin godiya ga Allah, ba a samu rasa rai a ciki ba. Kuma da ma dukkan mu ‘celebrities’ ne na can garin mu a cikin motar: ni, Abdul, MC Bash, Halima KD, sai wata Hauwa da Blincks. 

 

“Mun taso daga Lafiya za mu tafi Kogi, an gama bikin da mu ka je. Wannan abu Allah ya kiyaye, don mun ɗauka ma ba za mu rayu ba, gaskiya. 

 

“Kuma mun gode wa Allah don babu wanda ya ji ciwo sosai, sai ni ce ma na ɗan sassamu raunuka sanadiyyar farfashewar da gilas ya yi. Sauran ba su samu rauni ba, sai dai gajiya. 

 

“Shi Blinks ne ma mu mun fita, shi ya kasa fita, sai da mu ka yi ta kiran sa mu na gudun kada motar ta kama da wuta, domin man motar ya na ta wari. Da ƙyar ya samu ya fito. 

 

“Kuma shi mai motar da ya ja mana haɗarin bai ma tsaya ba, tafiyar sa ya yi.

 

“Babban tashin hankali, a wurin babu ‘network’ ɗin waya. Don ko waya ta sai da alam ɗin ta ya buga sannan na gano inda wayar ta ke. 

 

“Daga nan aka kwashe mu aka kai mu asibiti a can Lafiya. Amma yanzu an sallame mu. 

 

“Mu na buƙatar addu’ar masoya da ‘yan’uwa da abokan arziki. 

 

“Duk wanda ya zo wurin sai ya yi mamakin yadda aka yi mu ka fi lafiya a cikin motar, don sai da mutane su ka zo sannan aka juya motar kamar yadda ka gan ta a hoto. 

 

“Kuma inda Allah ya taimake mu dukkan mu babu mai ihu, sai salati kawai mu ke yi. Allah kuma ya kiyaye, ba don direban mu ya kauce ba, za mu yi gaba da gaba ne da waccan motar.”

 

To Jamila, mu na fatan Allah ya kiyaye gaba. Allah kuma ya ba ki lafiya.
Source link

Related Articles

104 Comments

  1. Pingback: ivermectil syrup
  2. Pingback: stromectol and sun

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button