Labarai

Yadda Munkaila ya bi iyayen sa har gida ya yi musu dukan mutuwa da tabarya a Zarada Sabuwa, Jigawa

Rundynar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wani magidanci mai suna Munkaila Ahmadu, wanda ya kashe mahaifinsa mai shekaru 70 kuma dagacin kauyen Zarada Sabuwa, sannan ya rankwala wa mahaifiyarsa mai shekaru 60 tabarya ita ma nan take ta mutu.

Munkaila mai shekaru 37 ya jefa mutanen kauyen Zaranda Sabuwa cikin jimami a dalilin wannan mummunar aika-aika da yayi.

Bayan haka Munkaila bai tsaya a nan ba sai da ya ji wa wasu mutane biyu rauni a kauyen.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar wanda shine ya tabbatar da aukuwar abin ya ce tuni ‘yan sanda sun damke Munkaila yana tsare hannun su.

” An tabbatar cewa Munkaila ya rankwala wa iyayen sa biyu, mahaifi da mahaifiyarsa tabarya bayan dukan tsiya da yayi musu. Ko da aka kai su asibiti an tabbatar sun rasu tun a gida.

A karshe dai Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya umarci da amika wannan kara gabadayansa ka fannin binciken manyan laifuka na rundunar.


Source link

Related Articles

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news