Labarai

Yadda mutanen Tangaza suka kutsa cikin ofishin ‘yan sanda suka fiddo ‘Yan bindiga suka babbake su

Jim kadan bayan ‘yan bindiga sun kashe wasu mutum biyu sannan sun yi garkuwa da wasu a garin Tangaza, jihar Sokoto, Jami’an ‘yan sanda da ‘yan banga sun bi sahun su inda suka kama wasu daga cikin su bayan sun yi arangama da wasu sun kashe mutum biyu.

Mazauna garin Tangaza, sun fusata bayan aukuwar abin suka taru da makaman su tare da yan sanda suka bi sahun maharan.

Cikin Ikon Allah kuwa sun samu nasarar cafke wasu mahara kusan 10 suka kuma kawo su ofishin ‘yan sanda.

Sai dai bayan ‘yan sanda sun kawo su ofishin su a Tangaza, sai mutanen gari suka dunguma ofishin ‘yan sandan domin suka bukaci ‘yan sandan su basu yan bindigan su kashe su kawai domin basu da amfani.

DPOn ‘Yan sandan ya ki yarda da wannan bukata ya amma kuma daga baya da suka nemi babbake ofishin ‘yan sandan, da karfin tsiya suka kutsa cikin ofishin suka fiddo su.

A karshe dai sun tara su waje daya suka babbake su kaf din su.


Source link

Related Articles

12 Comments

 1. Hello There. I found your blog using msn. This is a really
  well written article. I’ll make sure to bookmark it and come back to read more of your useful information. Thanks for the post.
  I’ll definitely comeback.

 2. With havin so much content do you ever run into any problems of plagorism or
  copyright violation? My blog has a lot of completely unique content I’ve either authored myself or outsourced
  but it looks like a lot of it is popping it up all over the internet
  without my agreement. Do you know any methods to help prevent content from being stolen? I’d really appreciate it.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button