Labarai

Yadda ’Yan bindiga suka sace sarki da dukkan ’yan majalisar sa kakaf

Wasu rikakkun ’yan bindiga sun yi awon-gaba da basarake sukutum da dukkan ‘yan majalisar Sarki baki daya, a jihar Imo.

An sace Sarki Charles Iroegbu, mai rike da sarautar Umuezie na Nguru, da ke Aboh Mbaise cikin Jihar Imo, a kan hanyar su ta komawa gida, bayan sun dawo daga wani shagalin daurin aure a masarautar Ihetti-Uboma.

An yi garkuwa da su a daidai ‘Seven and Half Junction’, cikin Karamar Hukumar Obowo.

Wanda ya ga yadda lamarin ya faru, ya bayyana cewa. “su dama masu garkuwar sun a bayan su ne, to da su ka wuce su, sai su ka tare hanya. Su ka fito su ka jefar da direban sarki waje, wani dan bindiga ya tuka motar da da kan sa, su ka arce.

Ratotanni sun tabbatar da cewa ‘yan majalisar sarki bakwai ne aka hada tare da basaraken aka yi garkuwa da su.

Matsalar tsaro na ci gaba da dagulewaa jihar Imo, inda baya ga sace basarake, an banka wa Hedikwatar ‘yan sandan jihar wuta, kuma aka fasa kurkukun Owerri.

Bayan nan kuma a cikin sa’o’i 72 an sake kai munanan hare-hare a ofisoshin ‘yan sanda guda biyu.

PREMIUM TIMES ta yi rahoton yadda yankin ya fara dagulewa a cikin wannan makon, a wani labari da ta bada yadda aka kai wa gidan kurkuku hari aka kubutar da daurarru 1,844.

Farmaki Kan Gidan Kurkukun Imo: Yankin Kudu-maso-Gabas da ya hada da jihohin Abia, Anambra, Enugu da Imo ya dagule tun bayan harin da aka kai wa Gidan Kurkukun Jihar Imo aka saki fursunoni kudan 2,000.

Dama kuma tun kafin wannan, an shafe shekaru ana fafatawa da tsagerun IPOB da sojoji, sannan kuma baya-bayan nan, IPOB sun kafa dakarun tsaro na ESN, wato Eastern Security Network, wadanda hususan ayyukan su ya jibinci korar Fulani makiyaya daga yankin da kuma kashe su, tare da kai wa Hausawa ‘yan tireda hare-hare.

Akalla mahara da su ka dira gidan kurkukun Imo da ke Owerri babban birnin jihar, sun saki fursunoni har 1,844, kamar yadda jami’an gidan kurkukun su ka tabbatar.

Wannan hari dai an zargi tsagerun IPOB, duk da dai kakakin yada labarai na Hukumar Gidan Kurkuku, Francis Enobore ya fitar da sanarwar cewa wasu ‘yan bindiga ne, amma bai furta sunan kungiyar IPOB ba.

“Sun yi nasarar shiga cikin gidann kurkukun da misalin karfe 9 na dare, ta hanyar fasa bango ta baya da nakiya.

Lokacin da ya yi sanarwar, a ce wasu shida sun koma, sannan wasu 35 sun ki ficewa.

Kai Wa Hedikwatar ’Yan Sandan Imo Hari:

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da cewa tsagerun IPOM ne su ka kai wa Hedikwatar ‘yan sandan jihar Imo hari. Kuma sun zarge su da kai hari gidan kurkukun jihar har su ka saki daurarru 1,844.

Kakakin ‘yan sanda Frank Mba ya ce ba a kashe dan sanda ko daya ba, amma wani ya ji rauni.

Amma hukumar ta dora laifin a kan IPOB da tsagerun tsaron kungiyar wato ESN.

“An kai harin tsakar daren Lahadi, kusan wajewar garin Litinin 5 Ga Afrilu, 2021 wajen karfe 9 na dare” Inji sanarwar kakakin ‘yan sandan Najeriya, wato daidai lokacin da aka kai farmaki gidan kurkukun jihar kenan.

Sufeto Janar Mohammed Adamu ya umarci Kwamishinan ‘Yan Sandan Jhar Imo ya gano wadanda su ka kai farmakin kuma a damke su.

Buhari Ya Yi Tir Da Hare-haren Kurkukun Imo Da Na Hedikwatar ’Yan Sandan Imo:

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da harin da wasu ‘yan bindiga su ka kai hedikwatar ‘yan sandan jihar Imo da kuma gidan kurkukun jihar, har su ka saki daurarru 1,844.

Tun bayan kai hare-haren dai jami’an ‘yan sandan kasar nan su ka dora alhakin a kan tsagerun IPOB da kuma bangaren tsaron su na ESN.

“A fushin da ya nuna tun da safiyar Litinin, Shugaba Buhari ya jinjina wa kokarin da jami’an tsaro su ka yi wajen hana masu harin kaddamar da kashe-kashe da lalata dukiya.”

Haka sanarwar da Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Garba Shehu ya bayyana a ranar Litinin.

Buhari ya nuna fushinn sa daga Landan inda ya je domin a duba lafiyar sa.

Buhari ya ce wannan farmaki ta’addanci ne, kuma ya gargadi dukkan bangarorin hukumomin tsaron yankin Kudu-maso-Gabas su tabbatar da sun binciko kuma sun kamo wadanda ke da hannu, sannan an hukunta su a kotu kamar yadda doka ta tabadar.

Hare-haren Imo: Gwamna Uzodinma Ya Kafa Kwamitin Bincike:

Gwamna Hope Uzordinma na Jihar Imo ya yi tir da hare-haren da aka kai Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar Imo da kuma Gidan Kurkukun Jihar da ke Owerri, babban birnin jihar. Ya ce hare-haren biyu dabbanci ne karara.

Ya yi wannan bayani bayan tashi daga taron Majalisar Tsaron Jihar Imo a Gidan Gwamnati, inda ya tattauna irin barnar da masu kai hare-haren su ka yi.

Dama kuma kafin sannan, sai da gwamnan ya ziyarci dukkan wuraren da aka kai wa munanan hare-haren.

Uzodinma ya ce ya kafa kwamitin da zai binciki lamarin kuma tabbas sai an hukunta dukkan masu hannu a kai hare-haren.

Idan Gemun Dan’uwan Ka Ya Kama Wuta: Jihar Abia Ta Sa Dokar Ta-baci A Wasu Garuruwa:

Ganin yadda lamari ya dagule a jihar Imo, hakan ya sa Gwamnatin Jihar Abia kakaba doka a babban birnin jihar Umuahia, da kuma Aba, birnin kasuwanci na yankin jihohin kabilun Ibo.

An kafa dokar hana zirga-zirgar ce dan lokaci kadan bayan da mahara da aka zarga tsagerun IPOB da ESN su ka kai mummunan farmaki da Hedikwatar ‘Yan Sandan Imo da kuma Gidan Kurkukun Jihar Imo a Owerri, har su ka saki fursunoni 1,844.

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Abia, John Kalu ne ya sanar da kakaba dokar hana zirga-zirgar a Aba da Umuahia.

Ya ce an hana zirga-zirga daga karfe 10 na dare zuwa karfe shida na safe, har zuwa yadda hali ya yi.


Source link

Related Articles

10 Comments

  1. 422400 767061Likely to commence a business venture about the refers to disclosing your products and so programs not just to individuals near you, remember, though , to several potential prospects much more via the www often. earn cash 251356

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news