Labarai

Yadda ‘Yan bindiga sun kashe malamin makaranta a jihar Nasarawa

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashi da makami sun kashe malamin makarantar sakandaren GSS mai suna Auta Nasela dake Nasarawa-Eggon a jihar Nasarawa.

Wani Malami a makarantar da baya so a fadi sunan sa saboda tsaro ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa maharan sun afka makarantar da misalin karfe 8 na yamman Asabar din makon jiya.

Ya ce ko da maharan suka dira makarantar sun wuce kai tsaye zuwa gidan Malam Nasela suk bukaci ya basu kudi.

“A guje Nasela ya fito gidan sa amma daya daga cikin maharan ya biyo sa ya harbe shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar’yan sandan jihar Ramhan Nansel ya tabbatar maharan ‘yan fashi da makami ne.

“Jiya da misalin karfe 8:45 mun samu labarin cewa ‘yan bindiga sun shiga makarantar GSS dake Nasarawa-Eggon inda suka kashe wani malamin makaranta mai suna Auta Nasela.

“Binciken da muka gudanar ya tabbatar mana cewa malamin ya yi kokarin Neman taimako daga makwabcinsa sai dai kafin ya kai gidan sa maharan suka kashe shi.

Nasel ya ce ‘yan sanda sun yi gaggwar kai Nasela asibiti inda a asibitin ya rasu yayin da likitoci ke duba shi.

Ya ce tuni rundunar ta fara gudanar da bincike domin kamo maharan.

Nasel ya yi kira ga mutane da su rika taimakawa wa jami’an tsaro da bayanan da suka san zai taimaka wajen dakile hareharen yan bindiga.


Source link

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news