Labarai

Yadda ‘Yan sanda suka ceto jariri daga hannun barauniyar Jarirai a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta damke wata mata da mijinta da suka hada baki suka sace jaririn wasu a asibiti, Abdullahi Wase dake Jihar Kano.

Abubakar Sadiq da matarsa Maryam Sadiq mazauna rukunin gidaje dake Rijiyar Zaki, jihar Kano.

Wani magidanci mai suna Rabi’u Muhammad ya kawo karar bacewar jaririn sa a asibitin Muhammaed Abdullahi Wase dake Nasarawa jihar Kano ofishin yan sanda.

An gano cewa maidakin Rabiu ta haifi tagwaye a asibitin. Surakar sa ta dauki daya tana raino sai barci ya kwashe ta a wajen zama a sibitin.

Ta farka ne ba ta ga jariri ba.

Kakakin ‘yan sandan jihar Kano Abdullahi Kiyawa ya bayyana cewa bayan an kawo karar bacewar jaririn ofishin yan sanda, suka fantsama aiki nemo wadanda suka sace jaririn. Ba su dade ba kuwa suka gano wadanda suka sace wannan jariri.

Maryar Sadiq ta shaida wa ‘yan sanda cewa mijinta Abubakar ne ya tilasta ta aikata wannan abu saboda tsananin neman da namiji da yake yi ruwa a jallo, Allah kuma bai bashi.

Ita Maryam Shekarar ta 22, Abubakar kuma shekara 50.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button