Labarai

Yahaya Bello ya siya fom din takarar shugaban Kasa na APC

Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya siya fom din takarar shugaban Kasa na APC.

Jam’iyyar APC ta sanar da saida fara saida form din ta na takarar kujeru tun a makaon jiya sai dai kuma bayan daga saida form din da ta yi an fara sai da shi a yau Talata.

Yahaya Bello tun da sanyin safiyar Talata ya garzaya hedikwatar jam’iyyar ya siya fom din.

Shine dankara na farko da ya fara siyan form din a cikin jerin yan takaran APC.

Darektan kamfen din Yahaya Bello Yemi Kolapo ya bayyana cewa hakan na nuni ne cewa gwamna Bello fa da gaske yake.

” Mun gama lissafin mu kaf, Yahaya Bello ne zai yi nasara a zaben saboda dinbin magoya baya da yake da su a fadin kasar nan musamman matasa.

Fom din Takarar APC

‘Yan Najeriya sun cika da mamaki ganin yadda jam’iyya mai mulki APC, ta yanka farashin fam ɗin takarar shugabancin ƙasa kan naira miliyan 100.

Hakan ya sa Premium Times ta yi ƙididdigar da ta nuna cewa kuɗin fam ɗin na takarar shugaban ƙasa sun zarce yawan albashin Shugaban Ƙasa kan sa na tsaron mulkin sa na shekaru bakwai.

Hakan ya sa jama’a na cike ta tambayar APC cewa ta yaya za ta bai wa mutum aiki amma kuma fam ɗin neman aikin ya fi tsadar albashin sa na shekara bakwai, ba ma na wata ɗaya ba?

Albashin Shugaban Ƙasa a Najeriya dai Naira miliyan 1.17 duk wata, ciki kuwa har da alawus-alawus ɗin sa. Amma tantagarya kuma gundarin albashin naira 292,892 ne. Sauran kuma duk alawus-alawus ne na haƙƙin aiki.

Haka albashin ya ke a Hukumar Raba Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa (RMAFC).

Ƙididdigar game-gari ta nuna albashin shugaban ƙasa a Najeriya Naira miliyan 14.05 a kowace shekara.

A cikin shekaru bakwai, Shugaban Ƙasa zai karɓi albashin naira miliyan 98.5.

A cikin shekaru huɗu, zai karɓi naira miliyan 56.2, kusan rabin kuɗin fam ɗin da ya saya na Naira miliyan 100 kenan.

Wato za ka sayi fam na Naira miliyan 100. Idan ka ci zaɓe, za a ba ka albashin shekaru huɗu na zangon shugaban ƙasa na farko.

Mutane da yawa fassara farashin fam ɗin da cewa wani salo ne na ɗaure wa satar kuɗin gwamnati gindi kawai.

Wasu kuma ganin cewa wani salo ne na hana wanda ba shi da ƙarfi fitowa ya nuna sha’awar tsayawa takarar shugabancin Najeriya.

Ga mai son tsayawa takara, banda kuɗin fam naira miliyan 100, akwai kuma gaganiyar kashe biliyoyin kuɗaɗe wajen kamfen yayin rangadin sassa, jihohi da yankunan karkara da sauran garuruwa.

Su na ɗaukar haya da shatar jiragen sama, ga kuɗaɗen kama otal-otal, ɗaukar ma’aikata, tallace-tallace, biyan mawaƙa, kama hayar gine-ginen ofisoshin ɗan takara a faɗin jihohin Najeriya da Abuja.

Sannan kuma akwai maƙudan kuɗaɗen da ake kashe wa wakilan jam’iyyar da za su yi zaɓe, wato ‘delegates’.

Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya yi alƙawarin daƙile cin hanci da rashawa tun kafin 2015, har yanzu bai ce komai ba, dangane da tsadar fam ɗin.

Hasali ma ya na zaune a Dakin Taro a otel ɗin Transcorp Hilton Hotel Abuja, Majalisar Zartaswa ta APC ta bayyana farashin fam ɗin naira miliyan 100.

A 2014, Buhari ya yi ƙorafi ganin cewa APC ta sayar da fam na takarar shugaban ƙasa, a kan naira miliyan 27.5. Buhari a lokacin ya ce fam ɗin ya yi matuƙar tsada. Har ya ce bashin banki ya ci sannan ya samu kuɗin sayen fam ɗin.

Hakan ya nuna farashin shiga takarar Shugaban Ƙasa a 2023, ya nunƙa na shekarar 2015 kusan da kashi 300%.

Har yanzu dai ɓangaren masu neman tsayawa takarar shugaban ƙasa daga ɓangaren APC babu wanda ya yi ƙorafin cewa fam ɗin ya yi tsada.


Source link

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news