Labarai

YAJIN AIKI: Gwamnatin Najeriya ta yi wa likitoci barazanar hana su albashi

Gwamnatin Tarayya ta yi barazanar tsaida albashin duk wani likitan da ya tsunduma yajin aiki tun a ranar Alhamis da ta gabata.

Ministan Kwadago Chris Ngige ne ya bayyana haka, cikin wata tattaunawa da ake yi da shi a gidan talbijin.

“Zuwa ranar Talaba zan sake gayyatar su mu sake zaunawa. Amma idan su ka kekasa kasa su ka ki janyewa din, zan nuna masu ba su isa ba.” Inji Minista Ngigel.

“Ai akwai wani makami a dokar aiki, wanda zan rika zabga masu duka da shi. Wato ‘idan ba ka yi aiki ba, to babu biyan ku albashi.”

Dokar aiki dai ta ce ko ma’aikata sun tafi yajin aiki, to wajibi ne a rika biyan su alabashi, matsawar a kungiyance su ka tafi yajin aikin.

Sai dai kuma dokar ta yi karin hasken cewa gwamnatin tarayya za ta iya dakatar da albashin wadanda su ka tafi yajin aiki, idan ta yi amanna cewa masu yajin aikin ba su da wani kwakkwaran dalilin daina aiki, kuma idan gwamnatin ta gamsu cewa yajin aikin haramtacce ne, ba shi da dalili.

Su dai likitocin Najeriya sun tafi yajin aiki saboda neman biya masu bukatun da su ka ce wajibi ne a biya masu.

Sun yi korafin ana wasa da rayukan su, kuma likitocin kungiyar NARD 17 sun mutu a Babban Asibitin Ibadan, yayin da a cikin Yuli, 2020 aka sanar cewa likitoci 812 su ka kamu da cutar korona.

Ita ma kungiyar Manyan Likitoci ta Kasa ta bayyana cewa mambobin kungiyar 20 cutar korona ta kashe a wurin kokarin su na ceton rayukan masu fama da cutar korona.

Haka kuma PREMIUM TIMES ta bada labarin cewa akalla aikin kula da masu cutar korona ya yi sanadiyyar kashe mana likitoci 17, shi ya sa muka shiga sahun yajin aiki –Shugaban Likitocin Badun

Shugaban Kungiyar Likitocin Babban Asibitin Jami’ar Ibadan (UCH), Temitope Husein, ya bayyana cewa sun shiga cikin sahun yajin aikin da uwar kungiyar su ta likitocin Najeriya NARD ta shirya, saboda likitoci abokan aikin su 17 ne su ka rasa rayuwar su sakamakon aikin kula da masu cutar korona.

Hussein a kokarin san a nuna wajibcin tafiyar da su ka yi yajin aiki a karkashin kuniyar likitoci ta kasa Nard, ya bayyana cewa tun bayan mutuwar likitocin 17, har yau iyalan su ba su samu kudaden inshora din da ake bai wa iyalan mamacin da ya mutu a wurin aiki ba.

Ya kara da cewa likitocin sun tafi yajin aiki ne domin neman a biya su hakkin su da aka danne wa wasu yan uwan su likitoci a kasar nan.

Hakkokin sun hada da albashin da wasu ke bi har yau ba a kai ga biyan su ba, sannan kuma akwai alawus-alawus da kuma bukatar da su ke da ita na kara masu alawus din saida rayukan su da su ke yi da sauran su.

Ya nuna matukar damuwa da korafin cewa wasu likitocin su na fama da kuncin rayuwa sakamakon kin biyan su albashi, tsawon watanni uku da har yau su ke jira, ba a biya su ba.

Hussein ya kara da cewa likitoci sun bai wa Gwamnatin Tarayya isasshen lokaci na watanni uku domin su duba lamarin naira 5,000 kacal da ake bai wa likita matsayin kudin alawus din saida rai da ya ke yi. Amma har yau ba a kara masu ba.

Ya nuna haushin cewa a baya sun bai wa gwamnati wa’adin kwanaki 60, amma ba ta yi komai ba. “Kuma tun a ranar 25 Ga Janairu wannan wa’adin ya kare. Mun tafi yajin aiki ne saboda aiki mu ke yi, amma babu lada, sannan babu Allah bada lada.” Inji Hussein.

PREMIUM TIMES ta buga labarin tafiya yajin aikin da likotocin Najeriya su ka yi, kwanaki biyu bayan Buhari ya tafi neman ta sa lafiyar a Landan.

Kungiyar Likitocin Najeriya ta shiga yajin aikin game-gari, kwana biyu bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi kasar Ingila domin ganin likitocin sa.

Kokarin da gwamnatin Tarayya ta yi domin shawo kan lamarin, ta hanyar kiran taron sasantawa da Ministan Kwadago, Chris Ngige ya yi da shugabannin kungiyar likitocin ta NARD a ranar Laraba, bai haifi da mai idanu ba, domin taron bai hana likitocin tafiya yajin aiki ba.

“Mun fara yajin aiki tun daga yau Alhamis karfe 8 na safe, yayin da a gefe daya kuma mu na nazarin tayin da gwamnatin tarayya ta yi mana”. Inji Shugaban Kungiyar Likitocin Najeriya, Uyilawa Okhuaiheuyi da a Turance a ke kiran ta da suna NARD.

Wannan furucin da ke sama, shugaban ya yi shi ne ga wakilin PREMIUM TIMES a safiyar Alhamis.

Muhammadu Buhari ya tafi Ingila, domin likitocin sa a Landan su duba lafiyar sa.


Source link

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button