Labarai

YAJIN AIKIN ƘUNGIYAR ƘWADAGO: Kotu ta ce kwamitin binciken da Gwamnatin Kaduna ta kafa haramtacce ne

Kotun Sauraren Ƙararrakin Biyan Haƙƙin Ma’aikata ta ce Kwamitin Bincike na Gwamnatin Kaduna kan Ƙungiyar ‘Yan Ƙwadago na jihar haramtacce ne.

Mai Shari’a Osatohanmwen Obaseki ne ya zartas da wannan hukunci a ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa Gwamna Nasir El-Rufai ba shi da ikon kafa wa ‘yan ƙwadagon jihar kwamitin binciken yajin aikin su na ranar 16 zuwa 19 Ga Mayu, 2021 da kuma binciken dukkan abin da ya biyo bayan yajin aikin.

Kotun ta ce tabbas Gwamna zai iya kafa Kwamitin Bincike, amma fa ba shi da ikon kafa kwamitin binciken ayyuka ko rikicin ƙungiyar ma’aikatan ƙwadago.

Haka nan kotun ta ce abubuwan da gwamnati ta lissafa wa kwamitin ya bincika duk sun danne haƙƙin da dokar ƙasa ta bai wa ma’aikatan ƙwadago. Saboda haka kwamitin haramtacce ce, ba shi da ikon yin wani bincike.

Kotu ta ƙara da cewa Gwamna El-Rufai ya yi tuwo na mai na, domin shi ya kafa kwamitin bincike, shi ya naɗa mambobin kwamitin, kuma ya umarce su shi za su kai wa sakamakon binciken da kwamitin ya yi. Hakan a cewa kotun ya nuna shi ne kuma zai hukunta su.

Mai Shari’a ta ce kwamitin haramtacce ne, domin Gwamna ya maida kan sa mai hukunta waɗanda ya ke gani da laifi, alhali kuma da shi ake tafka rikicin, wanda kusan saboda gwamnan ne ma ma’aikatan ƙwadagon jihar Kaduna su ka tafi yajin aikin.

Mai Shari’a ta ce Sashe na 6 da na 254 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da kuma Sashe na 20, 36 da na 40 na Dokar Kafa Ƙungiyoyin Ma’aikata sun rattaba cewa Kotun Sauraren Rikice-rikicen ma’aikata ce kaɗai za ta iya saurare ko yanke hukuncin ladaftarwa ga ma’aikatan ƙwadago.

Obaseki ta haramta wa Gwamna El-Rufai sake kafa wani kwamitin bayan wanda kotun ta ruguza.

Kuma ta haramta wa kwamitin binciken dalilan yin yajin aikin.

A ƙarshe kotu ta ci tarar Gwamnatin Jihar Kaduna Naira 500,000, waɗanda kotun ta ce a biya ƙungiyar ƙwadago, wadda ita ce ta kai gwamnatin Kaduna ƙara.


Source link

Related Articles

8 Comments

 1. Hi are using WordPress for your blog platform? I’m new to the
  blog world but I’m trying to get started and
  create my own. Do you require any coding knowledge to make your own blog?
  Any help would be really appreciated!

 2. Hello there! This post couldn’t be written much better!
  Going through this post reminds me of my previous roommate!
  He always kept preaching about this. I am going to forward this post to him.
  Fairly certain he’ll have a very good read. Thanks for sharing!

 3. Hello! I know this is kinda off topic but I was wondering which blog platform are you using for this site?
  I’m getting tired of WordPress because I’ve had problems with hackers and I’m looking at alternatives for another platform.
  I would be great if you could point me in the direction of a good platform.

 4. Having read this I thought it was very enlightening.
  I appreciate you finding the time and energy to put this short
  article together. I once again find myself
  spending way too much time both reading and posting comments.

  But so what, it was still worth it!

  Here is my web-site arrow metal sheds

 5. Thank you for every other informative site.
  Where else may just I am getting that type of info written in such an ideal approach?

  I’ve a mission that I am simply now operating on, and I have been on the look out for such information.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

Adblock Detected

Please turn off your ad blocker so that we can earn something and you get more news