Labarai

’Yan bindiga sun nausa daji da Kakakin Yada Labaran Hukumar Shige-da-fice

An sanar da cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Kakakin Yada Labarai ta Hukumar Jami’an Shige-da-fice ta Jihar Edo, mai suna Bridget Esene.

An yi garkuwa da ita a ranar Lahadi, a lokacin da ta ke kan hanyar ta zuwa coci, domin yin ibadar karshen mako.

An ce mahara din sun rika bin ta ne tun daga unguwar su da ke cikin babban birnin jihar Edo, su ka ritsa ta kan hanya, daga nan kuma su ka rika jan ta a kasa, har su ka jefa ta a cikin motar su kuma su ka arce da ita.

” Har yanzu ba san inda ta ke ba, kuma wadanda su ka gudu da ita ba su kira waya su na neman diyya ba.

“Amma dai an tsinci motar ta a kan hanyar Agbor Road, inda aka bar motar bayan sun yi awon gaba da ita. Kuma an hakkace cewa bayan sun jefa ta a mota, sun kama hanyar garin Auchi ne a guje.”

Haka dai wani jami’in da ya nemi a sakaya sunan sa ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Shi ma Kakakin Yada Labarai na Yan Sanda a Edo, Chidi Nwabuzor, ya ce ba shi da masaniya a batun, don haka ba shi da iznin cewa komai tukunna.


Source link

Related Articles

86 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button